APC a Ingila: Kanzon kuregene, ba a yi zanga-zangar adawa da Buhari a kasar Landan ba

APC a Ingila: Kanzon kuregene, ba a yi zanga-zangar adawa da Buhari a kasar Landan ba

- Jam'iyyar APC ta karyata hotunan da ke yawo ana ikirarin zanga-zangar nuna adawa da Buhari a Landan

- Jam'iyyar ta bayyana asalin inda aka dauko hotunan, tare da bayyana ranan da aka daurasu

- Hakazalika ta shawarci wanda ya watsa hotunan cewa ya sani wannan zunzurutun karya ne

Jam’iyyar APC reshen kasar Ingila, ta karyata wani labarin karya na kafofin sada zumunta cewa wasu ‘yan Najeriya sun mamaye gidan da shugaba Buhari yake a Landan don nuna adawa da Shugaban.

Jaridar Punch a jiya ta ruwaito cewa shugaban ya tashi daga Najeriya zuwa Landan inda zai kwashe makonni biyu domin duba lafiyarsa.

Wani a dandalin Twitter, @Tqswaggerboi, ya watsa hotunan wasu masu zanga-zanga tare da ikirarin cewa suna jiran isowar Buhari Fadar Najeriya ne a Landan.

KU KARANTA: Jami'an kwana-kwana uku da wasu sun jikkata a wata gobara a Kaduna

APC a Ingila: Kanzon kuregene, ba a yi zanga-zangar adawa da Buhari a kasar Landan ba
APC a Ingila: Kanzon kuregene, ba a yi zanga-zangar adawa da Buhari a kasar Landan ba Hoto: bellanaija.com
Source: UGC

“Daruruwan masu zanga-zanga da asalinsu 'yan Najeriya ne sun mamaye Fadar Najeriya da ke Landan, suna jiran isowar Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ke zuwa ziyarar duba lafiya na makonni biyu. #BuhariMustGo," ya sanya tare da hotunan.

A martanin da ta mayar game da hotunan, APC ta ce, "Don Allah ka sani cewa @Tqswaggerboi rubutunka na karfe 7.54 na safe LABARIN KARYA ne!"

Jam'iyyar ta watsa likau zuwa gidan yanar gizon da aka samo hotunan, wanda ke nuna cewa ba kwanan nan aka dauke su ba, asalinsu daga sigar Burtaniya ta zanga-zangar #EndSARS ta Oktoban bara ne.

KU KARANTA: Najeriya da Dubai sun bankado masu turowa 'yan Boko Haram kudade daga waje

A wani labarin, A ranar Laraba, 31 ga watan Maris ne wasu ’yan asalin Najeriya mazauna kasar Birtaniya, suka gudanar da zanga-zanga a kan Shugaba Muhammadu Buhari, inda suka nemi ya koma gida.

Sashin Hausa na BBC ta ruwaito cewa wasu ’yan Najeriya a Birtaniya sun taru a kofar gidan Gwamnati Najeriya da ke birnin Landan sannan kuma suka tare hanyar shiga ciki.

Masu zanga-zangar sun kasance dauke da kwalaye inda suka rika kira ga Shugaban kasar na Najeriya da ya koma kasarsa yayin da suka yi cincirindo a bakin Asibitin Wellington da ke birnin Landan.

Source: Legit

Online view pixel