Yanzu-yanzu: Buhari ya ba da umarnin murkushe 'yan fashi, masu satar mutane

Yanzu-yanzu: Buhari ya ba da umarnin murkushe 'yan fashi, masu satar mutane

- Shugaba Buhari ya fadawa shugabannin hafsoshin sojan kasar da su fatattaki ‘yan fashi da masu daukar nauyinsu daga kasar

- Shugaban ya bayyana hakan ne a ranar Talata, 30 ga watan Maris, a Aso Rock- Buhari ya ce gwamnatin sa ba za ta sake lamuntan ayyukan 'yan fashi a cikin kasar ba

- Buhari ya ce gwamnatin sa ba za ta sake lamunta da ayyukan 'yan fashi a cikin kasar ba

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci shugabannin hafsoshin tsaro da sauran jami'an tsaro da na leken asiri da su gano tare da fitar da 'yan fashi, masu satar mutane da masu daukar nauyinsu.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Manjo-Janar Babagana Monguno, ne ya bayyana hakan ga manema labarai na fadar shugaban kasa.

Ya fadi hakan ne bayan taron tsaro, wanda Shugaba Buhari ya jagoranta a fadar gwamnatin, Abuja.

Yanzu-yanzu: Buhari ya ba da umarnin murkushe 'yan fashi, masu satar mutane
Yanzu-yanzu: Buhari ya ba da umarnin murkushe 'yan fashi, masu satar mutane Hoto: @NGRPresident
Asali: Twitter

KU ARANTA KUMA: APC ta yi ikirarin cewa ba ta taba sanin matakin da cin hanci da rashawa ya kai ba a Najeriya

Legit.ng ta tattaro cewa shugaban ya kuma gargadi shugabannin tsaro cewa a halin da masu aikata laifuka ke sanin hanzarin lamuran tsaro a kasar ya kamata a kawo karshen su nan take, tare da umartar su dauki mataki.

Jaridar TheCable ta ruwaito cewa ya kara da cewa shugaba Buhari ya kuma dage cewa duk shawarar da aka amince da ita a taron majalisar tsaron kasa da aka gudanar kwanan nan, gami da hana ayyukan hakar ma'adanai a Zamfara da kuma dokar hana-tashi, su ci gaba da aiki har sai baba ta gani.

Ya ambato shugaban yana cewa ya kamata sojojin su kara kaimi maimakon yin dauki-ba-dadi.

Monguno ya ce shugaban ya kuma dage cewa duk shawarar da aka amince da ita a taron majalisar tsaron kasa da aka yi a watan Fabrairu ta ci gaba da aiki.

Shawarwarin sun hada da hana ayyukan hakar ma'adanai a Zamfara da kuma dokar hana jirgi tashi da aka sanya wa jihar.

KU KARANTA KUMA: Na kashe mahaifiyata saboda fasto ya ce mun mayya ce, ‘yar shekara 30

An ruwaito shugaban yana cewa ya kamata abubuwa su ci gaba da kasancewa a haka a jihar Zamfara, ta yadda za a dakile rashin tsaro a jihar.

A baya mun ji cewa, Shugaba Muhammadu Buhari na jagorantar zaman tsaro a cikin fadar Aso Villa yanzu haka.

Ana zaman ne yayinda shugaban kasan ke shirin tafiya Landan, kasar Ingila domin duba lafiyarsa.

Daga cikin wadanda ke zaman akwai mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo; Sakataren gwamnatin jihar Boss Mustapha; Ministan tsaro, Bashir Salihi Magashi; shugaban ma'aikatar fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari; da mai bada shawara kan tsaron kasa, Babagana Monguno.

Asali: Legit.ng

Online view pixel