Shugaban Majalisa ya roki Shugaba Buhari ya jarraba shawarwarin da Tinubu ya bada
- Femi Gbajabiamila ya yi magana a wajen bikin Bola Tinubu colloquium 12
- Bola Tinubu ya fadawa gwamnati yadda za ta gyara tsaro da tattalin arziki
- Shugaban majalisar ya yi kira ga gwamnati ta duba shawarwarin Tinubu
Shugaban majalisar wakilan tarayya, Femi Gbajabiamila, ya fito ya yi magana bayan Bola Tinubu ya bada shawarwarin magance matsalolin da ake fama da su.
Rt. Hon. Femi Gbajabiamila ya yi kira ga gwamnatin Muhammadu Buhari ta duba shawarwarin da Bola Ahmed Tinubu ya bada, sannan kuma ta yi aiki da su.
Jaridar Daily Trust ta ce Femi Gbajabiamila ya bayyana hakan ne ta bakin hadiminsa, Lanre Lasisi.
KU KARANTA: Daga cikin APC Tinubu zai gamu da cikas a 2023 - Hadimin Jonathan
Mista Lanre Lasisi ya ce Femi Gbajabiamila ya na ganin akwai abubuwan da za a dauka a jawabin da Bola Tinubu ya yi a wajen bikin cikarsa shekara 69 da aka yi.
Da yake magana wajen wannan biki na mauludin Bola Tinubu, wanda shi ne na 12 a tarihi, Gbajabiamila ya ce za a iya dabbaka wasu shawarwarin na Tinubu.
Ya ce: “Yau mun saurare shi ya yi jawabi, kuma mun dauki darasi daga abubuwan da mu ka ji.”
Rt. Hon. Gbajabiamila ya cigaba da cewa: “Ina so in ce mu jarraba wadanan shawarwari (na Tinubu) a aikace domin abubuwanmu su dawo daidai a Najeriya.”
KU KARANTA: Hazo ya hana manyan baki zuwa bikin da aka shiryawa Tinubu
Gbajabiamila ya halarci bikin ne ta kafar taro ta yanar gizo ta Zoom. Shugaban majalisar wakilan ya na cikin wadanda hazo ya hana jirginsu zuwa garin Kano a jiya.
Har yanzu gwamnatin tarayya ba ta ce uffan game da shawarwarin da aka ba ta ba. A na sa jawabin, shugaban kasa ya yi magana ne kan muhimmancin hadin-kai.
Idan ku na biye da mu, kun ji cewa jagoran na jam'iyyar APC, Bola Tinubu ya na so gwamnati ta daina tsuke aljihu, sannan a tura matasa miliyan 50 zuwa aikin Sojoji.
Tsohon gwamnan na jihar Legas ya bada shawarar gwamnati ta dumbuza kudi a gari saboda a zaburar da tattalin arziki, ganin yadda ake fama da fatara a kasar nan.
Asali: Legit.ng