Abin da ya hana Osinbajo, SGF, Ministoci, zuwa gagarumin bikin da aka shiryawa Bola Tinubu

Abin da ya hana Osinbajo, SGF, Ministoci, zuwa gagarumin bikin da aka shiryawa Bola Tinubu

- Manyan bakin da aka gayyata zuwa bikin Bola Tinubu ba su samu zuwa ba

- Yanayin gari ya hana jiragen sama tashi daga Garin Abuja zuwa jihar Kano

- Hazo ne ya kawowa Yemi Osinbajo, Boss Mustapha, da wasu Ministoci cikas

Bikin da aka shirya domin taya jagoran jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu murnar cika shekara 69 da haihuwa ya gamu da cikas a ranar Litinin.

Punch ta samu labari cewa matsalar yanayi da ake fama da shi ya jawo da-dama daga cikin wadanda su ka shirya zuwa bikin su ka gagara zuwa Kano.

Jaridar ta ce dole ta sa manyan mutanen da su ka yi shirin zuwa wannan gagarumin taro su ka fasa.

KU KARANTA: A dauki matasa miliyan 50 aikin soja - Tinubu

Wadanda wannan matsala ta shafa su ne; mai girma mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha.

Sauran wadannan manyan mutane sun hada da Ministoci irinsu Ministan yada labarai da al’adu, Lai Mohammed, da na harkar cikin gida, Rauf Aregbesola.

Mai magana da yawun mataimakin shugaban kasa, Laolu Akande, ya yi magana ta shafinsa na Twitter, ya ce mai gidansa ba zai samu halartar taron ba.

Hakan ya sa sai dai Yemi Osinbajo ya halarci bikin ta kafar yanar gizo da tare da shugaban kasa.

KU KARANTA: Tinubu ya yabi Ganduje a kan yaki da rashin gaskiya

Abin da ya hana Osinbajo, SGF, Ministoci, zuwa gagarumin bikin da aka shiryawa Bola Tinubu
Bola Tinubu Colloqium
Asali: Facebook

Ya kamata a ce an fara bikin ne da karfe 12:00 na rana, amma aka daga zuwa 12:30 na ranan saboda manyan bakin da aka gayyata su samu damar halarta.

Wanda aka ba nauyin gabatarwa ya bada wannan sanarwa a shafin taron yanar gizo na Zoom.

Amma duk da haka ana sa ran cewa shugaban masu rinjaye a majalisar tarayya, Ado Doguwa, ya jagoranci ‘yan majalisa 60 na jihar Kano zuwa wajen taron.

Babban Jigon PDP kuma kusa a gwamnatin PDP da su ka shude, Doyin Okupe, ya yarda Bola Tinubu abin tsoro ne, amma ya ce zai tika shi da kasa a zaben 2023.

Tsohon mukarrabin na Dr. Goodluck Jonathan ya na hangen kujerar shugaban kasa, kuma ya sha alwashin rankwala Tinubu da kasa idan su ka hadu a filin zabe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel