Kwana 2 bayan gyara wutan Maiduguri, yan Boko Haram sun sake lalatawa

Kwana 2 bayan gyara wutan Maiduguri, yan Boko Haram sun sake lalatawa

Kimanin awanni 48 bayan gyara wutan birnin Maiduguri da kamfanin TCN tayi, yan ta'addan Boko Haram sun sake lalata wayoyin isar da lantarki na Damaturu-Maiduguri.

Daily Trust ta ruwaito cewa wani babban jami'in TCN ya tabbbatar da hakan da yammacin Asabar.

"Bayan kokarin da kamfanin TCN tayi na gyara wutan lantarkin Maiduguri, birnin jihar Borno, yan ta'addan sun sanya Bam a layin wutan 152 da 153 (Molai) 330kv dake Damaturu-Maiduguri misalin karfe 5:56 na safiyar 27 ga Maris, 2021, inda suka jefa garin Maiduguri cikin duhu karo na biyu," jami'in ya bayyana.

Kwana 2 bayan gyara wutan Maiduguri, yan Boko Haram sun sake lalatawa
Kwana 2 bayan gyara wutan Maiduguri, yan Boko Haram sun sake lalatawa
Asali: Facebook

Wannan ba shine karo na farko da yan ta'addan Boko Haram zasu jefa mutan Maiduguri cikin duhu ba.

A watan Junairu, yan ta’addan Boko Haram sun lalata wani layin da ya jawo lantarki zuwa cikin jihar Borno.

Harin na ranar 26 ga watan Junairu shine na uku a cikin watan wanda mayaƙan dake ikirarin kafa ƙasar musulunci (ISWAP) ta kai garin, kuma ya yi sanadiyyar ɗaukewar wutar gaba ɗaya.

Amma da yammacin Laraba, 24 ga Maris, mazauna garin Maiduguri sun ɓarke da murna da da suka ga hasken wutar lantarki ya dawo a yankin su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng