Ana kuka bayan ‘Yan ta’adda sun datse layin da ya shigo da wuta garin Maiduguri

Ana kuka bayan ‘Yan ta’adda sun datse layin da ya shigo da wuta garin Maiduguri

- Tabargazar ‘Boko Haram ta kai ga lalata layin wutar da ya shigo Borno

- Lalata wutar lantarki da Boko Haram su ka yi, ya jawo ana zama a duhu

- Ba wannan ne karon fari da ‘Yan ta’addan su ka yi irin wannan aiki ba

Mutanen garin Maiduguri da kewaye su na zaune a cikin duhu bayan ‘yan ta’addan Boko Haram sun lalata wani layin da ya jawo lantarki zuwa cikin jihar Borno.

Hukumar dillacin labarai na kasa, NAN ta rahoto cewa mutane sun zauna na tsawon mako guda babu wuta a sakamakon wannan barna da ‘yan ta’addan su ka yi.

NAN ta ce kasuwancin mutane da dama ya tsaya cak a sanadiyyar katse wutar lantarkin da aka yi. Rahoton ya ce masu amfani da na’urori kadai aka bari suna aiki.

Wasu mazauna babban birnin garin na Maiduguri da su ka yi magana da manema labarai sun koka game da yadda hukuma su ka gagara gyara masu wutar lantarkin.

KU KARANTA:Siyasa ta sa Buratai su ka gaza - Gwamna Wike

“Mako daya kenan, kusan babu wanda ya san abin da ya sa babu wuta a Maiduguri.

Mu na bukatar mu san abin da ya jawo wannan, da kuma kokarin da kamfanonin wuta su ke yi na magance matsalar.

Ba za ku bar jama’a a duhu ba tare da bayani ba. “inji wani mazauna mai suna Ibrahim Abubakar.

Wani bawan Allah mai amfani da wuta wajen sana’ar walda, Moses Bala, ya ce aikinsa ya tsaya cak. “Yanzu mako daya kenan babu wutar lantarki, ba na aiki.”

Musa Idris, Sahabi Abdulrahman, Amina Bello da Talatu Musa duk sun koka a lokacin da aka zanta da su, suka ce ba su san me ya kawo matsalar a Maiduguri ba.

Ana kuka bayan ‘Yan ta’adda sun datse layin da ya shigo da wuta garin Maiduguri
Sababbin shugabannin hafsun sojoji Hoto: Femi Adesina
Asali: Facebook

KU KARANTA: Akwai bambanci tsakain wannan Buharin da wanda na san - Obasanjo

Da aka tuntubi kamfanin Yola Electricity Distribution Company (YEDC) da ke bada wuta a Borno, Yobe, Adamawa da Taraba, sun ce matsalar ta na wajen TCN.

Wannan ne karo na biyu a cikin watanni biyu da ‘yan ta’addan su ka jawo matsalar wuta a Borno.

A karshen makon nan mun ji cewa sojojin kasan Najeriya tare da hadin-kan dakarun MNJTF sun yi raga-raga da wasu jagororin Boko Haram da ake ji da su.

Hakan na zuwa ne bayan nadin da wani shugaban Boko Haram ya yi, ya jawo rikicin cikin gida, wanda ya yi sanadiyyar aka yi masa juyin mulki a tafkin Chadi.

Sojojin MNJTF sun yi samame a ranar Juma’a, 29 ga watan Junairu, 2021, inda su ka samu galaba a kan wasu mayakan Boko Haram da jagororinsu a garin Bama.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng