Haske Yadawo a Maiduguri Bayan Wata Biyu da 'Yan Boko Haram suka saka garin a Duhu

Haske Yadawo a Maiduguri Bayan Wata Biyu da 'Yan Boko Haram suka saka garin a Duhu

- Wasu mazauna garin Maiduguri sun ɓarke da murna daga ganin hasken wutar lantarki yadawo yankin su.

- Yan ta'addan Boko Haram ne dai suka fatattaka hanyoyin raba wutar lantarkin wanda hakan yasa suka rasa ta na tsawon lokaci

- Ganin wutar ya basu mamaki kuma sun yi murna matuka, Sun yi kira ga gwamnati ta samar musu da tsaro a yankin su.

Mazauna garin Maiduguri sun ɓarke da murna da yammacin Laraba sa'ilin da suka ga hasken wutar lantarki ya dawo a yankin su, Channels TV ta ruwaito.

An rasa wutar lantarki a garin Maiduguri tin bayan wani hari da 'yan Boko Haram suka kai garin, suka yi fata-fata da hanyoyin da ke rarraba lantarkin.

Harin na ranar 26 ga watan Junairu shine na uku a cikin watan wanda mayaƙan dake ikirarin kafa ƙasar musulunci (ISWAP) ta kai garin, kuma ya yi sanadiyyar ɗaukewar wutar gaba ɗaya.

KARANTA ANAN: ‘Yan sanda sun cafke wani mai POS wanda ke taimakawa masu satar mutane wajen karbar kudin fansa

A kan wata hanya dake kusa da Bakassi, wanda ke ɗauke da mutane kimanin 30,000 waɗanda rikici ya rabo su da gidajensu, mazauna wajen na ta murnanr ganin hasken wutar lantarki yadawo.

"Tabbas ina matuƙar farin ciki da naga wutar lantarki ta dawo," inji Sihiniya Chinde, wacce ke zaune a kan wani benci, tana shirya girkin shinkafa da wake bayan taga hasken lantarkin yadawo.

"Ni ɗalibar lissafi da ƙididdiga ce, yanzun zan yi karatu na cikin kwanciyar hankali basai nayi amfani da cocila ba," injita.

A gaba ɗaya kan hanyar, akwai wasu yara dake siyo ruwan sanyi suna siyarwa a cikin wata ƴar jaka don samun na kashewa.

"Hasken wutar lantarkin ya dawo ne da misalin ƙarfe 5:42 na yamma," a cewar wani mai shago, Ibrahim Mustafa Goni.

Haske Yadawo a Maiduguri Bayan Wata Biyu da kawo harin 'Yan Boko Haram
Haske Yadawo a Maiduguri Bayan Wata Biyu da kawo harin 'Yan Boko Haram Hoto: @kedcoplc
Asali: Twitter

Kamfanin wutar lantarkin bai ce komai ba har yanzun, amma sun bayyana cewa suna kan aiki wajen ganin sun gyara hanyoyin rarraba wutar da zai bawa birnin dake ɗauke da mutane miliyan uku.

"Rayuwa ta yi wahala musamman lokacin zafi, lokacin da ake matuƙar buƙatar ruwa mai sanyi," inji wani ɗan shekara 48.

KARANTA ANAN: 'Yan bindiga sun nemi a biya kudin fansan wadanda suka sace a Abuja har N200m

A satin da ya gabata, gwajin yanayin garin yakai 42 digiri. Goni na tayar da inji daga ƙarfe shida na safe zuwa ƙarfe 10 na ɗare, wanda hakan na laƙume masa ƙuɗi kimanin N6,000 kullum.

Yace: "Na ƙara ma kayayyakin da nike siyarwa kuɗi wanda hakan yasa kwastomomina na ƙorafi."

"Amma ina farin ciki da dawowar wutar lantarki kuma ina kira ga gwamnati ta ƙara dagewa wajen samar mana da tsaro," a cewarshi.

ISWAP da Boko Haram na harin lalata duk wasu abubuwan more rayuwa a yankin, suna lalata wuraren kafar sadarwa da hanyoyin raba wutar lantarki a arewa maso gabas.

A wani labarin kuma 'Yan Bindiga sun hallaka wani Sufeton 'yan sanda, Sun babbaka motarsu a Delta

Wasu 'yan bindiga sun farmaki yan sanda ya yin da suke tsakar sintiri a garin Ashaka, karamar hukumar Ndokwa, jihar Delta.

- Maharan sun hallaka wani ƙaramin sufeta sannan suka babbaka ma motar yan sandan wuta.

Ahmad Yusuf sabon ma'aikacin legit.ng ne ɓangaren Hausa, ya fara aiki kwa nan nan. Yana kawo rahotanni a ɓangare daban-daban.

Ya yi karatun digirinsa na farko a Jami'ar kimiyya da fasaha dake garin wudil jihar Kano . Kuma yana da burin ƙwarewa a aikin jarida.

Za'a iya samunsa a dandalin sada zumunta na twitter @ahmadyusufmuha77 .

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel