FG ta roƙi Ƙungiyoyin Ƙwadugon Ƙasar nan da su Taimaka kada su Shiga yajin Aiki

FG ta roƙi Ƙungiyoyin Ƙwadugon Ƙasar nan da su Taimaka kada su Shiga yajin Aiki

- Gwamnatin tarayya ta roƙi haɗakar ƙungiyoyin ƙwadugo na kasar nan da kada su tsunduma yajin aiki kamar yadda suke shirin yi

- Ministan ƙwadigo na ƙasar ne ya bayyana haka a ya yin ƙaddamar da majalisar bada shawarwari kan ayyukan ƙungiyoyin ƙwadigo (NLAC)

- Ƙungiyoyin ƙwadigon na shirin shiga yajin aiki ne matuƙar ba'a watsar da kudirin dake gaban 'yan majalisar wakilai ba

Gwamnatin tarayya ta roƙi haɗakar ƙungiyoyin ƙwadigon ƙasar nan da kada su shiga yajin aikin da suke shirin yi a kan kudirin mafi ƙarancin albashi dake gaban majalisa.

Ministan ƙwadigo na ƙasar nan, Sanata Chris Ngige, ya yi wannan roƙon a wajen ƙaddamar da majalisar bada shawarwari kan ayyukan ƙungiyar ƙwadigo a Owerri, jihar Imo.

KARANTA ANAN: An ba da belin mawakin yabo da ya sake wakar yabo da ba a tantance ba

Taron wanda Mataimakin shugaban Ƙasa Prof. Yemi Osinbajo ne ya ƙaddamar dashi ta hanyar amfani da fasahar zamani (Virtually) a madadin shugaba Buhari.

Lokacin da yake jawabin ƙaddamarwa, Chris Ngige, ya ce yana goyon bayan haɗakar ƙungiyoyin ƙwadigo kan ƙin amincewa da shirin majalisa.

Amma ya roƙe su da kada su tsunduma yajin aiki domin hakan zai shafi cigaban ƙasa.

FG ta roƙi Ƙungiyoyin Ƙwadugon Ƙasar nan da su Taimaka kada su Shiga yajin Aiki
FG ta roƙi Ƙungiyoyin Ƙwadugon Ƙasar nan da su Taimaka kada su Shiga yajin Aiki Hoto: @SenChrisNgige
Asali: Twitter

Ƙudirin, wanda ke gaban 'yan majalisar wakilan ƙasar nan na ƙunshe da buƙatar a sake yiwa mafi ƙarancin albashi kwaskwarima, wanda hakan zai rage ƙarfin yarjejeniyar da aka cimma kan mafi karancin albashin.

Ministan ya ƙara da cewa, ba a buƙatar ƙungiyon su gode masa kan matsayar daya ɗauka akan kudirin domin shi kawai ya maimaita matsayar gwamantin tarayya ne.

A bayanin ministan yace:

"Duk da cewa wannan majalisar bata aiki na wani lokaci, amma ma'aikatar mu ta kiyaye dokar sauraron koke daga ɓangarori uku.

"Misali lokacin da muka tattauna akan mafi ƙarancin albashi, munyi amfani da tsarin zama da ɓangarori sama da uku waɗan da suka haɗa da; Gwamnati, ma'aikata, masu ɗaukar aiki, da kuma masu buƙatar shiga taron dan kansu." injishi.

KARANTA ANAN: Fitaccen dan siyasar PDP a Kudu maso Yamma ya mutu a hatsarin mota

"Amma a ɓangaren masu son shiga taron dan kansu munfi mai da hankali akan yan majalisar ƙungiyar nan ta ƙwadugo da aka ƙaddamar yanzu," inji Ministan.

Shugaban ƙungiyar ma'aikatan Najeria (NLC) Ayuba Wabba ya yabawa shugaban ƙasa muhammadu Buhari da ya saka NLAC a cikin doka, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Anashi bangaren shugaban yan kasuwa na ƙasar nan (TUC) wanda mataimakinsa, Quadri Olaleye ya wakilta ya yabawa ministan kasancewar sa namijin gaske kan aikinsa, amma yace zasu cigaba da abinda yakamata har sai komai ya dai-daita.

A wani labarin kuma Sanatoci sun Amince da naɗa Kwamishinan Hukumar Kula da Ma'aikatan Gwamnatin tarayya

Majalasar ta amince da naɗin nashi ne bayan duba rahoton Da kwamitin ta ya kawo a zaman majalisar na yau Talata.

Shugaban kwamitin Malam Ibrahim Shekarau ya bayyana basu sami wata matsala ko laifi da shi wanda ake son naɗawa yayi ba.

Ahmad Yusuf sabon ma'aikacin legit.ng ne ɓangaren Hausa, ya fara aiki kwa nan nan. Yana kawo rahotanni a ɓangare daban-daban.

Ya yi karatun digirinsa na farko a Jami'ar kimiyya da fasaha dake garin wudil jihar Kano . Kuma yana da burin ƙwarewa a aikin jarida.

Za'a iya samunsa a dandalin sada zumunta na twitter @ahmadyusufmuha77.

Asali: Legit.ng

Online view pixel