An ba da belin mawakin yabo da ya sake wakar yabo da ba a tantance ba
- Biyo bayan kame shi, kotu a jihar Kano ta bada belin shahararren mawakin yabo Bashir Dandago
- An kame Bashir Dandago da laifin sakin wata wakar yabo da hukumar tacewa ta jihar ba ta tace ba
- An bada belinsa akan kudi N500,000 tare da gabatar da manyan mutane biyu da zasu tsaya masa
Wata Babbar Kotun Majistare da ke zama a Kano, ranar Talata ta ba da beli kan kudi N500,000 ga wani shahararren mawakin yabo na Kano, Bashir Dandago, bisa zargin sakin wata waka da ba a tantance ta ba, Daily Nigerian ta ruwaito.
Da yake yanke hukunci, Babban Alkalin Kotun, Aminu Gabari, ya bayar da belin wanda ake kara a kan kudi N500,000, tare da gabatar da amintattun mutane biyu.
Ya ce daya daga cikin wadanda za su tsaya masa dole ya kasance Babban Kwamandan Hisbah a karamar hukumar Gwale ta jihar sannan na biyun ya zama dagacin unguwa ko mahaifin wanda ake karan.
Mista Gabari, daga nan sai ya dage zaman zuwa 13 ga Afrilu, domin ci gaba da sauraron karar.
KU KARANTA: 'Yan bangan Amotekun sun sake kame wasu shanu sama da 300
Tun da farko, dan sanda mai gabatar da kara, Aminu Kawu, ya fadawa kotu cewa an karbi karar ta aikata lafin kai tsaye da wanda ake zargin yayi daga Hukumar Kula da Tace Finafinai da Bidiyo na Jihar Kano a ranar 22 ga Maris.
Wanda ake tuhumar ya fitar da wata waka da ba a tantance ba, mai taken: “Hassada Ga Mallamai” (wakar da ka iya tunzura malamai a jihar).
Sai dai wanda ake tuhumar ya musanta aikata laifin.
A cewar mai gabatar da karar, laifin ya sabawa sashi na 112 na dokar lasisin finafinai na hukumar tacewa da ba da lasisi ta jihar Kano na shekarar 2011.
Lauyan wanda ake kara, Rabiu Abdullahi, ya gabatar da neman belin, a bisa sashi na 35 da 36 na kundin tsarin mulkin 1999 (wanda aka yi wa kwaskwarima) da kuma Sashe na 168,172, da kuma 175 na Dokar Aikata Laifuka, 2019.
Ya tabbatar wa kotun cewa idan har aka bayar da belinsa, wanda yake karewa ba zai wahala a binciken da ake ba.
KU KARANTA: Buhari ya karbo bashi daga waje don tallafawa masu kananan masana'antu
A wani labarin, Hukumar tace fina-finai ta jihar Kano, a ranar Litinin ta kama fitaccen mai wakokin yabon Annabi Muhammadu SAW, Bashir Dandago.
An kama shi ne kan zargin fitar da wakar da hukumar ta ce na iya tada fitina, da ta ce ya zagi malamai a jihar Kano kan matayarsu game da rikicin Sheikh AbdulJabbar Kabara.
Shugaban hukumar, Ismail Na'abba Afakallah ya tabbatarwa Daily Trust kamun.
Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.
Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.
A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.
Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez
Asali: Legit.ng