Yanzu Yanzu: Fitaccen dan siyasar PDP a Kudu maso Yamma ya mutu a hatsarin mota

Yanzu Yanzu: Fitaccen dan siyasar PDP a Kudu maso Yamma ya mutu a hatsarin mota

- Jihar Ondo ta yi rashin daya daga cikin tsoffin ‘yan majalisar ta, Akpoebi Lubi, sakamakon hatsarin mota

- Lubi ya rasa ran sa ne a ranar Talata, 23 ga Maris, bayan afkuwar abin takaicin

- Kafin rasuwarsa, marigayi dan majalisar ya kasance tsohon shugaban marasa rinjaye a majalisar dokokin jihar

Rahotanni sun kawo cewa Honarabul Akpoebi Lubi, tsohon shugaban marasa rinjaye na majalisar dokokin jihar Ondo, ya mutu bayan ya yi hatsarin mota.

Hadimin Sanata Nicholas Tofowomo wanda Lubi ya yi aiki a karkashin sa ne ya tabbatar da wannan mummunan lamarin wanda ya faru da yammacin ranar Talata, 23 ga watan Maris, jaridar The Nation ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Yaro dan shekara 13 ya burge mutane da dama a shafukan sada zumunta bayan ya kera abin hawa da kwalin sabulu

Yanzu Yanzu: Fitaccen dan siyasar PDP a Kudu maso Yamma ya mutu a hatsarin mota
Yanzu Yanzu: Fitaccen dan siyasar PDP a Kudu maso Yamma ya mutu a hatsarin mota Hoto: Sahara Reporters
Asali: UGC

Har zuwa lokacin mutuwarsa na ba zato ba tsammani, Lubi ya kasance mashawarci na musamman ga Tofowomo kan dabaru da maslaha ta musamman.

Kasancewar ya wakilci mazabar Ese-Odo a lokacin gwamnatin Olusegun Mimiko, tsohon dan majalisar ya kasance dan jam'iyyar PDP daya tilo da aka zaba a Majalisar a 2011.

A cewar jaridar Punch, mamacin ya kasance tsohon shugaban rikon kwarya na karamar hukumar Ese-Odo.

KU KARANTA KUMA: Sojoji zasu kafa aikin sintiri a Tyomu bayan harin da aka kaiwa Ortom

A wani labarin kuma, Shugaban riko na kwamitin tsare-tsaren babban taron kasa na jam'iyyar APC kuma gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya ce jam'iyyar na kokarin ganin ta ci gaba da mulki a kalla na tsawon shekaru 32, Daily Nigerian ta ruwaito.

Mista Buni ya bayyana hakan ne lokacin da yake kaddamar da kwamitin tuntuba da dabaru na jam’iyyar na mambobi 61, a Sakatariyar APC ta Kasa, da ke Abuja, a ranar Talata.

A cewarsa, ya kamata jam'iyyar ta kasance a kan mulki don ci gaba da samar da romon dimokiradiyya da take gabatarwa tun daga shekarar 2015.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Online view pixel