Matar Da Za Ta Auri Sojan Saman Da Aka Kashe a Kaduna Ta Auri Yayansa

Matar Da Za Ta Auri Sojan Saman Da Aka Kashe a Kaduna Ta Auri Yayansa

- Matar da aka saka wa rana da wani sojan Nigeria da ya rasu a watan Fabarairu ta auri yayansa

- Hakan ya faru ne bayan rasuwar marigayi Abubakar a ranar 13 ga watan Fabarairu yayin artabu da yan bindiga

- Duba da cewa saura makonni uku a daura aure Abubakar ya rasu, amaryar ta auri yayan marigayin

Matar da aka saka wa rana da Sojan Saman Nigeria da aka kashe a watan Fabrairu a Kaduna yayin artabu da yan bindiga ta auri yayansa kamar yadda LIB ta ruwaito.

Marigayi M. Abubakar na cikin sojojin saman Nigeria, NAF, da suka riga mu gidan gaskiya yayin artabu da yan bindiga a Unguwan Laya kusa da Birnin Gwari a ranar Asabar 13 ga watan Fabrairu.

Matar Da Za Ta Auri Sojan Saman Da Aka Kashe a Kaduna Ta Auri Yayansa
Matar Da Za Ta Auri Sojan Saman Da Aka Kashe a Kaduna Ta Auri Yayansa. Hoto: @lindaikeji
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Matasan Arewa Sun Bawa Sunday Igboho Wa'adin Awa 72 Ya Kwashe Yarbawa Daga Arewa

An yi jana'izarsa a Unguwan Dosa a karamar hukumar Kaduna ta Arewa ranar Lahadi 14 ga watan Fabarairu.

Marigayin ya wallafa hotunan kafin aurensa da aka yi shirin daura wa a watan Maris a shafin sada zumunta na Facebook.

KU KARANTA: Yadda Ma'aikatan Banki Ke Taimakawa Wajen Almundahana, Barrista Albashir Lawal Likko

A ranar Asabar 20 ga watan Maris na shekarar 2021, amaryar ta auri yayansa kamar yadda rahoton LIB ya nuna.

A wani rahoton, kun ji Rundunar yan sandan jihar Sokoto, a ranar Alhamis, ta ce ta kama a kalla mutane 17 kan zargin fashi da makami, garkuwa da mutane da wasu laifuka a jihar.

Mr Kamaldeen Okunlola, kwamishinan yan sandan jihar ne ya sanarwar manema labarai hakan a Sokoto, Vanguard ta ruwaito.

Okunlola ya ce rundunar a ranar 4 ga watan Maris ta kama wani Jabbi Wanto kan hadin baki da sace mutane biyu a Tamba Garka a karamar hukumar Wurno na jihar.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164