ASUP Za Ta Fara Yajin Aiki Na Ƙasa a Ranar 6 Ga Watan Afrilu

ASUP Za Ta Fara Yajin Aiki Na Ƙasa a Ranar 6 Ga Watan Afrilu

- Kungiyar malaman kwallejin fasaha na kasa, ASUP, ta yi barazanar fara yajin aiki a ranar 6 ga watan Afrilu

- Shugaban kungiyar na kasa, Anderson U Ezeibe ne ya sanar da haka bayan taron kungiyar da aka gudanar a Katsina

- ASUP ta yi zargin gwamnatin tarayya ba ta kulawa da bukatun kungiyar duk da sun dade suna gabatarwa gwamnatin korafe-korafensu

Kungiyar malaman kwallejin fasaha na kasa, ASUP, ta sanar da fara yajin aiki na kasa daga ranar 6 ga watan Afrilun 2021 kan zargin 'rashin kulawa da gwamnati ke yi game da batutuwan da suka shafi ilimin fasaha a kasar, The Nation ta ruwaito.

Shugaban ASUP, Anderson U Ezeibe ya shaidawa manema labarai a karshen taron kungiyar karo na 99 da aka gudanar a Hassan Usman Polytechnic da ke Katsina cewa sun shiga yajin aikin yin ne saboda wasu muhimman abubuwa shida da ke addabar ilimin kwallejin fasaha.

ASUP Za Ta Fara Yajin Aiki Na Ƙasa a Ranar 6 Ga Watan Afrilu
ASUP Za Ta Fara Yajin Aiki Na Ƙasa a Ranar 6 Ga Watan Afrilu. Hoto: @TheNationNews
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Samia Hassan: A Karon Farko, An Rantsar Da Mace Matsayin Shugabar Kasa a Tanzania

Ya bayyana cewa gwamnati ta dade tana watsi da bukatun kungiyar a shekarun da suka gabata.

A cewarsa, matsalolin sun hada da rashin aiwatar da yarjejeniyar ASUP/FG na shekarar 2010, rashin biyan albashi da ariyas da rashin aiwatar da sabbin albashi mafi karanci a wasu kwallejin jihohi da sauransu.

Ya ce duk da cewa kungiyar ta yi taro da gwamnatin tarayya a watan Oktoban 2020 a kan wasu batutuwa, kungiyar ta ce har yanzu gwamnati ba ta aiwatar da abubuwan da suka amince da su ba.

KU KARANTA: Shaidar EFCC: Lamiɗo Ya Rika Karbar Cin Hanci Daga Hannun Ƴan Kwangila Lokacin Yana Gwamna

Kungiyar ta kuma lissafa wasu ka'idoji 10 da za a cika musu kafin su janye yajin aikin da za su fara a ranar 6 ga watan Afrilu da suka hada da aiwatar da shawarwarin da ke cikin rahoton NEEDS na shekarar 2014, kafa kwamitin kula da kwallejin fasaha da sauransu.

A wani rahoton daban kun ji cewa, rundunar yan sandan jihar Kano ta kwantar da jama'a hankula game da wasu bakin mutane tare da rakuma da suka bayyana a wasu sassan jihar.

Daily Nigerian ta gano cewa mazauna jihar sun ankarar da yan sanda kan bakin mutanen da suka yada zango a wasu sassan jihar.

Wasu mazauna garin suna zargin matafiyar sun iso jihar ne domin aikata laifi da sunan fataucin kanwa.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Online view pixel