Samia Hassan: A Karon Farko, An Rantsar Da Mace Matsayin Shugabar Kasa a Tanzania

Samia Hassan: A Karon Farko, An Rantsar Da Mace Matsayin Shugabar Kasa a Tanzania

- An rantsar da Samia Sulhu Hassan a matsayin shugaban kasa mace ta farko a kasar Tanzania

- An yi bikin rantsarwa ne a yau Juma'a 19 ga watan Maris na shekarar 2021 a birnin Dar es Salaam

- Samia Hassan ta samu dare wa kujerar shugabancin kasar ne bayan rasuwar Shugaba John Pombe Magufuli

An ranstar da Samia Suluhu Hassan a ranar Juma'a a matsayin mace ta farko a matsayin shugaban kasar Tanzania bayan rasuwar John Magufuli bayan fama da rashin lafiya.

Hassan, mai shekaru 61, kuma musulma daga Zanzibar za ta karasa wa'addin mulkin Magufuli na biyu kafin ta yi takara a shekarar 2025.

DUBA WANNAN: Raba Gardama: Gwamnatin Kwara Ta Ce Dalibai Musulmi Na Iya Saka Hijabi a Dukkan Makarantunta

Samia Hassan: A Karon Farko, An Rantsar Da Mace Matsayin Shugabar Kasa a Tanzania
Samia Hassan: A Karon Farko, An Rantsar Da Mace Matsayin Shugabar Kasa a Tanzania. Hoto: @MobilePunch
Source: Twitter

Sanye da dan kwali mai launin ja, an rantsar da Hassan a matsayin shugaban kasa na shida a wani biki da aka yi a Dar es Salaam inda mafi yawancin wadanda suka hallarci taron ba su saka takunkumin fuska ba a kasar da ke shakka game da cutar korona.

DUBA WANNAN: Hijabi: Idan Rikici Ya Barke, Gwamnan Kwara Za a Tuhuma, Kungiyar CAN

"Ni, Samia Suluhu Hassan, na yi alkawarin biyayya da kare kundin tsarin mulkin Tanzania," a cewar sabuwar shugaban kasar a yayin da ta ke rantsuwar kama aiki kafin ta duba dakarun sojojin kasar da suka yi mata faretin ban girma.

A halin yanzu ita ce shugaban kasa mace da ke kan mulki a nahiyar Afirka sai kuma Sahle-Work Zewde ta kasar Ethiopia wacce ba shugaba bane mai cikaken iko.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel