Shaidar EFCC: Lamiɗo Ya Rika Karbar Cin Hanci Daga Hannun Ƴan Kwangila Lokacin Yana Gwamna

Shaidar EFCC: Lamiɗo Ya Rika Karbar Cin Hanci Daga Hannun Ƴan Kwangila Lokacin Yana Gwamna

- Shaidar hukumar EFCC ya yi ikirarin cewa tsohon gwamnan jihar Jigawa Sule Lamido da yaransa sun karbi cin hanci daga hannun yan kwangila

- Shaidan mai suna Micheal Wetkas ya bada wannan bayanin ne yayin da ya bayyana a gaban kotu da ke sauraron tuhumar almundahar kudi da ake yi wa tsohon gwamnan

- Tun a shekarar 2015, hukumar EFCC ta taba kama Lamido tare da yaransu biyu kan zargin almundahar kudade da rashawa

Michael Wetkas, wani shaidar hukumar yaki da rashawa ta EFCC, ya yi zargi tsohon gwamnan jihar Jigawa Sule Lamido da karbar cin hanci daga hannun yan kwangila da ake bawa aiki a lokacin mulkinsa, rahoton The Cable.

A shekarar 2015, hukumar EFCC ta kama tsohon gwamnan tare da yaransa biyu, Aminu da Mustapha kan zargin almundahar kudade da rashawa.

Shaidar EFCC: Lamido Ya Rika Karbar Cin Hanci Daga Hannun Yan Kwangila Lokacin Yana Gwamna
Shaidar EFCC: Lamido Ya Rika Karbar Cin Hanci Daga Hannun Yan Kwangila Lokacin Yana Gwamna. Hoto: @thecableng
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Raba Gardama: Gwamnatin Kwara Ta Ce Dalibai Musulmi Na Iya Saka Hijabi a Dukkan Makarantunta

Daga baya an gurfanar da su a wata kotun tarayya da ke Abuja.

A shekarar 2018, EFCC ta sake gurfanar da su ukun a kan zargin damfarar jihar Jigawa kudi har Naira biliyan 1.35.

A ranar Alhamis, Wilson Uwujaren, kakakin EFCC, ya ce yayin zaman kotun shaidar EFCC ta fada wa kotu yadda wadanda ake karar suka yi amfani da kamfanoninsu wurin karbar cin hanci daga yan kwangila.

Ya ce an bada kwamgilolin ne a lokacin da Lamido ke gwamnan jihar Jigawa.

Wetkas ta hanyar amfani da hotuna ya nuna wa kotun yadda kamfanoni kamar su Dantata and Sawoe Construction Company, Interior Woodworks Ltd., da A.G Ferrero & Co Ltd suka rika tura kudi asusun ajiyar banki na Lamido da yaransa karkashin kamfaninsa na Bamaina Holdings Ltd. da Speeds International Ltd.

KU KARANTA: Hijabi: Idan Rikici Ya Barke, Gwamnan Kwara Za a Tuhuma, Kungiyar CAN

Alkalin da ke shari'ar, Ijeoma Ojukwu ta dage cigaba da sauraron karar har zuwa watan Mayun 2021 domin bada damar yi wa shaidar tambayoyi.

Lamido, tsohon ministan harkokin kasashen waje ya yi gwamna a jihar Jigawa daga shekarar 2007 zuwa 2015.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Online view pixel