Abubuwa 10 da ya kamata ka sani a kan Macen farko da za ta zama Shugabar kasar Tanzania

Abubuwa 10 da ya kamata ka sani a kan Macen farko da za ta zama Shugabar kasar Tanzania

- Kasar Tanzaniya ta samu macen farko a matsayin Shugaba a karon farko

- Samia Suluhu Hassan ce za ta gaji John Magafuli da ya mutu a kan mulki

- Mun tsakuro takaitaccen tarihin Hon. Suluhu daga shafin Standard Media

Kasar Tanzaniya za ta koma hannun Samia Suluhu Hassan a daidai lokacin da ake makokin shugaba John Pombe Magufuli wanda ya rasu a ranar Laraba.

Doka da tsarin mulkin Tanzaniya sun ba mataimakiyar shugaban kasa, Samia Suluhu Hassan cikakken ikon hawa kujerar tun da shugaban kasar ya rasu.

1. A shekarar 2020 Samia Hassan ta shiga siyasa, ta samu kujerar majalisar wakilai a Zanzibar.

2. Shugaban kasar Zanzibar na wancan lokaci, Amani Karume, ya ba ta kujerar Ministar tarayya.

3. A ranar 5 ga watan Nuwamban 2015 ne Samia Hassan ta zama mataimakiyar shugabar kasar Tanzaniya.

KU KARANTA: Gwanda da akuya ‘sun kamu’ da COVID-19 a Tanzaniya

4. A lokacin da marigayi John Pombe Magufuli ya dauko Hon. Samia Hassan, ta na rike ne da kujerar karamar Ministar da ke kula da harkokin kungiyoyi na kasar.

5. Tsakanin 2010 da 2015, Samia Suluhu ta zama Ministar kasuwanci, hannun jari da sha’anin yawon buda ido.

6. Har ila yau, Hon. Suluhu ta rike kujerar Ministar harkokin mata da cigaban yara a gwamnatin baya.

7. Suluhu ta na auren Hafidh Ameir, wani tsohon Malamin gona, kuma sun haifi ‘ya ‘ya uku.

8. ‘Diyar ta mace, Mwanu Hafidh Ameir, ta bi sahunta, yanzu haka ta na majalisar wakilan Zanzibar.

KU KARANTA: Shugaban Tanzania ya goyi bayan malamai su rika dukan dalibai

Abubuwa 10 da ya kamata ka sani a kan Macen farko da za ta zama Shugabar kasar Tanzania
Samia Suluhu Hassan Hoto: africafeeds.com
Asali: UGC

9. Kafin Samia Suluhu Hassan, babu macen da ta taba rike kujerar shugaba a Tanzaniya, alal hakika a kaf Afrika ta gabas, ba a taba samun mace da ta yi mulki ba.

10. Hon Samia Suluhu Hassan za ta shafe shekara biyar ta na kan mulki a matsayin shugabar kasa ta shida a kasar Tanzaniya, ita ce macen farko a wannan kujera.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Online view pixel