Gwanda da akuya ‘sun kamu’ da COVID-19 a Tanzania

Gwanda da akuya ‘sun kamu’ da COVID-19 a Tanzania

Shugaban Tanzania, John Magufuli ya bayyana damuwarsa game da naurorin gwajin kwayar cutar COVID-19 da aka sayarwa kasarsa bayan an yi wa gwanda da akuya gwajin kuma sakamakon ya nuna sun kamu da corona.

A cewar Aljazeera, Magafuli, wanda ya yi jawabi a ranar Lahadi a wani taro a Chato, arewa maso yammacin kasarsa ya ce ya umurci a fara bincike a kan ingancin naurar gwajin.

An ruwaito cewa sun dauki samfurin gwaji daga wasu ababen da ba dan adam ba kamar akuya, tinkiya da gwanda.

Sannan aka saka wa samfurin sunayen mutane da shekaru aka tura wa dakin gwajin kwayar cutar da corona da ke kasar domin ayi gwajin ba tare da masu gwajin sun san ainihin inda aka debo samfurin ba.

Gwanda da Akuya ‘sun kamu’ da COVID-19 a Tanzania

Gwanda da Akuya ‘sun kamu’ da COVID-19 a Tanzania
Source: UGC

DUBA WANNAN: Ban alakanta mace-macen Kano da korona ba - Dr Gwarzo

A cewar shugaban kasar, sakamakon da aka fitar ya nuna cea gwanda da akuya suna dauke da kwayar cutar.

Magafuli ya ce akwai yiwuwar an samu kuskure ne yayin gudanar da gwajin.

Ya ce lamarin ya nuna cewa akwai yiwuwar a iya sanar da cewa wasu mutane sun kamu da cutar duk da cewa a zahiri ba su dauke da ita.

"Akwai abinda ke faruwa. Kamar yadda na taba fada a baya, ba kowanne tallafi da ake bamu bane alheri ga kasar nan," in ji shi.

Wannan na zuwa ne a lokacin da shugaban kasar ya bayar da umurnin a siyo maganin coronavirus na gargajiya da ake zaton za ta iya kashe kwayar cutar da COVID-19 daga Madagascar duk da cewa masanna kimiyya ba su gwada maganin ba.

Ya ce, "Na riga na rubuta wa shugaban kasar Madagascar wasika kuma nan ba da dade wa ba za mu aika da jirgin sama domin ya kwaso mana magungunan domin Tanzania ta amfana da shi."

A halin yanzu dai akwai mutane 480 da suka kamu da cutar a kasar inda mutum 16 sun mutu kamar yadda worldometers.info ta ruwaito.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Online view pixel