Shugaban Tanzania ya goyi bayan malamai su rika dukan dalibansu

Shugaban Tanzania ya goyi bayan malamai su rika dukan dalibansu

- Shugaban kasar Tanzania, John Magufuli ya jinjinawa wani gwamnan kasar da ya zane yara 'yan makaranta

- Ana zargin yaran da kona wajen kwanansu ne a matsayin maida martani bayan da malaminsu ya kwace musu wayar tafi da gidanka

- Magufuli ya ce, yaso a dakatar da yaran daga karatu har sai iyayensu sun biya asarar da suka yi, kuma a mika masu hannu tsundum a aika-aikar gidan gyaran hali

Shugaban kasar Tanzania, John Magufuli ya jinjinawa gwamnan wani yanki akan zane yara 'yan makaranta 14, ya ce dama ya yi fiye da hakan.

Faifan bidiyon da ya dinga yawo a yanar gizo ya nuna Albert Chalamila, gwamnan Mbeya a kudancin Tanzania, yana dukan yaran makaranta bayan da suka kwanta a kasa.

Sun taka dokar makaranta ne inda suka aka hana su zuwa da wayoyi sai suka kone wajen kwanansu don maida martani.

An ladaftar dasu ne a gaban dalibai, 'yan sanda da malamai; hakan kuwa ya jawo cece-kuce a kafofin yada labarai.

KU KARANTA: Abin Mamaki: Alkali ya harbe kansa ana tsaka da shari'a

"Ina taya kwamishinan yankin murna sakamakon zane daliban da ya yi amma hakan bai isa ba. Da ya yi fiye da hakan," in ji shugaban kasar a ranar Alhamis yayin da ya kai ziyawa ga yankin da ke da makwaftaka da yankin makarantar.

"Wasu mutane na maganar hakkin dan Adam amma babu yadda za a yi mu samu yara masu gadara. Bai kamata su kona wajen kwanansu ba saboda malamai sun kwace wayoyin da aka hanasu amfani da su,"

"Na sanar da kwamishinan yankin cewa ya dakatar da duk daliban makarantar kuma sai iyayensu sun biya asarar sannan a barsu su dawo makaranta. Wadanda kuwa aka kama da hannu dumu-dumu, a mikasu gidan gyaran hali."

A dokar ta 1979, ladaftarwa aiki ne na shugaban makaranta kuma sai a manyan laifuka. Ladaftarwar kuwa ta kunshi zana ne a hannu ko a mazaunai.

Ladaftarwa a makarantu ta jawo hargitsi a shekarar da ta gabata inda aka samu malami da ya raunata yaro mai shekaru 13 a yankin arewacin Kagera inda har dai yaron ya rasa ransa.

Masu kare hakkin bil adama sun ce ladaftarwa ta yi yawa a makarantun kasar Tanzania. A don haka ne aka bukace hanawa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel