Wakili: Kotu Ta Tura Ƴan Kungiyar OPC Uku Zuwa Gidan Gyaran Hali Kan Zargin Kisa

Wakili: Kotu Ta Tura Ƴan Kungiyar OPC Uku Zuwa Gidan Gyaran Hali Kan Zargin Kisa

- Wata kotu da ke zamanta a Ibadan ta bada umurnin ajiye ƴan kungiyar Yarbawa ta OPC su uku a gidan gyaran hali

- Rundunar Ƴan sanda ta gurfanar da mutanen uku ne kan zargin hadin baki, kisa da ƙona gida

- Alƙalin kotun ya umurci rundunar yan sanda ta mika takardar karar ga DPP don neman shawarar Shari'a

Wata kotun Majistare da ke zamanta a Ibadan a ranar Laraba ta bada umurnin ajiye mambobin kungiyar Oodua People's Congress (OPC) a gidan gyaran hali kan zargin yin ƙone-ƙone, The Nation ta ruwaito.

An sanda sun gurfanar da mutane uku masu suna Awodele Adedigba, 45; Dauda Kazeem, 38 da Hassan Ramon kan zargin laifin hadin baki, kisan kai da ƙone-ƙone.

Wakili: Kotu Ta Tura Ƴan Kungiyar OPC Uku Zuwa Gidan Gyaran Hali Kan Zargin Kisa
Wakili: Kotu Ta Tura Ƴan Kungiyar OPC Uku Zuwa Gidan Gyaran Hali Kan Zargin Kisa. Hoto: @MobilePunch
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Yanzu-Yanzu: ICPC Ta Kama Tsohon Shugaban JAMB Kan Almundahar N900m

Alƙalin kotun, Mr Olaide Hamzat, bai saurari Shari'a wadanda ake zargin ba a yanzu ya bada umurnin a ajiye su a gidan gyaran hali ta Abolongo da ke Oyo.

Hamzat ya umurci yan sanda su kai takardar karar zuwa ofishin DPP don neman shawara ta Shari'a.

Tunda farko, ɗan sanda mai shigar da ƙara Opeyemi Olagunju ya shaidawa kotu cewa a ranar 7 ga watan Maris misalin ƙarfe 8 na safe a ƙauyen Kajola, Ayete, ya yi sanadin rasuwar wata mai shekaru 45.

KU KARANTA: An Rasa Rayuka Sakamakon Hatsarin Da Trela Dauke da 'Yan kasuwa 70 Ta Yi a Bauchi

Ya ce Awodele da Dauda da Hassan sun cinna wuta a gidan Abdullahi Wakili da aka ƙiyasta kudinta ya kai miliyan biyar.

Ya ce laifin ya ci karo da sashi na 316, 324, 443 da 516 na masu laifuka na jihar Oyo, 2000.

Idan za a iya tunawa wata kotun a ranar Talata ta bada umurnin a tsare Wakili a gidan gyaran hali.

Yan sanda na zargin Wakili da ƴaƴansa uku da laifin hadin baki, garkuwa da mutane da fashi.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel