Yanzu-Yanzu: ICPC Ta Kama Tsohon Shugaban JAMB Kan Almundahar N900m

Yanzu-Yanzu: ICPC Ta Kama Tsohon Shugaban JAMB Kan Almundahar N900m

- Hukumar ICPC ta kama, Farfsesa Dibu Ojerinde, tsohon shugaban hukumar shirya jarrabawar shiga jami'o'i, JAMB

- Ana zargin Farfesa Ojerinde ta laifuka masu alaka da almundaha da bannatar da kudade har N900m

- Hukumar ta ICPC ta ce za ta gurfanar da shi a kotu ta zarar ta kammala bincike a kansa

Hukumar Yaki da rashawa ta ICPC ta kama tsohon Rajistara kuma shugaban hukumar shirya jarrabawar shiga jami'o'i, JAMB, Farfesa Dibu Ojerinder kan zarginsa da bannatar da Naira miliyan 900.

Ana zargin Ojerinde da aikata laifuka na almundaha yayin da ya ke shugabancin hukumar JAMB da Hukumar Shirya Jarrabawar Kammala Sakandare ta Kasa, NECO, rahoton The Nation.

DUBA WANNAN: Sayyada Rabi'atu Harun: Matar Da Ta Yi Waƙar 'Mai Daraja Annabi Ma'aiki' Ta Rasu

Yanzu-Yanzu: ICPC Ta Kama Tsohon Shugaban JAMB Kan Almundahar N900m
Yanzu-Yanzu: ICPC Ta Kama Tsohon Shugaban JAMB Kan Almundahar N900m. Hoto: @TheNationNews
Asali: Twitter

An kama shi ne a ranar 15 ga watan Maris na 2021 a babban birnin tarayya, Abuja kamar yadda kakakin hukumar ICPC, Mrs Azuka C. Ogugua ta sanar.

Sanarwar ta ce, "Hukumar ta tsare Ojerinde domin amsa tambayoyi kan almundahar kudi, kaucewa biyan haraji, amfani da ofishinsa ba bisa ka'ida ba da yi wa jami'an gwamnati karya.

"An kuma zargi tsohon shugaban na JAMB da bada kwangiloli ga kamfanonin bogi da aka kasa gano su.

"Ana zargin ya bada kwangilar siyo fensir da kilina a kan N450 kowannensu ga wasu kamfanoni masu suna Double 07 Concept Limited da Pristine Global Concept Limited, tsakanin 2013 da 2014 yayin da ya ke shugabancin hukumar JAMB.

KU KARANTA: Jerin ƙasashen Afirka 7 da kuɗaɗensu ya fi daraja a 2021

"Babu hujjar cewa an siyo kayan da aka bada kwangilarsu da ya kamata a yi amfani da su yayin jarrabawa kuma ba a ga yan kwangilar ba.

"An bada wasu kwangiloli masu kama da wannan ga kamfanonin Solid Figures Limited, Holywalk Limited da wasu kamfanonin kan kudade ba tare da ganin kwangilar ba.

"Ana rike da Farfesa Ojerinde bayan samun izinin alkali kuma za a gurfanar da shi a kotu da zarar an kammala bincike."

A wani rahoton daban kun ji cewa, rundunar yan sandan jihar Kano ta kwantar da jama'a hankula game da wasu bakin mutane tare da rakuma da suka bayyana a wasu sassan jihar.

Daily Nigerian ta gano cewa mazauna jihar sun ankarar da yan sanda kan bakin mutanen da suka yada zango a wasu sassan jihar.

Wasu mazauna garin suna zargin matafiyar sun iso jihar ne domin aikata laifi da sunan fataucin kanwa.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Online view pixel