An Rasa Rayuka Sakamakon Hatsarin Da Trela Dauke da 'Yan kasuwa 70 Ta Yi a Bauchi

An Rasa Rayuka Sakamakon Hatsarin Da Trela Dauke da 'Yan kasuwa 70 Ta Yi a Bauchi

- Wasu yan kasuwa da suka fito daga garin Darazo a jihar Bauchi sun yi hatsarin mota

- Hatsarin ya faru ne a hanyarsu na zuwa kasuwar Dukku da ke jihar Gombe a safiyar yau

- Hukumar FRSC reshen jihar Bauchi ta tabbatar da afkuwar hatsarin inda ta ce a kalla mutum shida sun rasu

Hatsarin mota ya ritsa da yan kasuwa fiye da 70 a hanyar Darazo-Dukku inda mutane shida suka riga mu gidan gaskiya, The Punch ta ruwaito.

An ruwaito cewa yan kasuwan da ke cikin trela sun fito daga garin Darazo ta karamar hukumar Darazo a jihar Bauchi suna hanyarsu ta zuwa kasuwar Dukku a jihar Gombe a safiyar yau Laraba a lokacin da hatsarin ya faru.

An Rasa Rayyuka Sakamakon Hatsarin Da Trela Dauke da 'Yan kasuwa 70 Ta Yi a Bauchi
An Rasa Rayyuka Sakamakon Hatsarin Da Trela Dauke da 'Yan kasuwa 70 Ta Yi a Bauchi. Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Sayyada Rabi'atu Harun: Matar Da Ta Yi Waƙar 'Mai Daraja Annabi Ma'aiki' Ta Rasu

Kwamandan Hukumar Kiyayye Haddura ta Kasa, FRSC, na jihar Bauchi, Yusuf Abdullahi ya tabbatar wa wakilin majiyar Legit.ng hakan cikin hirar wayar tarho.

Ya ce jami'an na FRSC sun yi aiki matuka wurin ceto wadanda hatsarin ya ritsa da su inda ya ce a halin yanzu ba a tantance wadanda suka mutu ba.

Abdullahi ya ce, "Eh, an yi hatsari a safiyar yau da ya ritsa da mutum fiye da 70 da ke cikin trela da ke hanyarta na zuwa kasuwar Dukku.

"Motar ta kauce daga hanya ta yi watsi da mutanen da ke cikinta. Wasunsu sun makale cikin motar, mun kwashe awanni muna kokarin ceto su, yanzu ana tantance su.

KU KARANTA: Jerin ƙasashen Afirka 7 da kuɗaɗensu ya fi daraja a 2021

"Ba zan iya fada maka takamammen adadin wadanda suka rasu ba amma wasu daga cikin yan kasuwan sun mutu. Da zarar mun kammala tantancesu, zan baka cikakken bayani kan lamarin."

A wani rahoton daban kun ji cewa, rundunar yan sandan jihar Kano ta kwantar da jama'a hankula game da wasu bakin mutane tare da rakuma da suka bayyana a wasu sassan jihar.

Daily Nigerian ta gano cewa mazauna jihar sun ankarar da yan sanda kan bakin mutanen da suka yada zango a wasu sassan jihar.

Wasu mazauna garin suna zargin matafiyar sun iso jihar ne domin aikata laifi da sunan fataucin kanwa.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: