Yanzu-Yanzu: Majalisar Wakilai Ta Kafa Kwamiti Mai Ƙarfi Kan Tsaro

Yanzu-Yanzu: Majalisar Wakilai Ta Kafa Kwamiti Mai Ƙarfi Kan Tsaro

- Majalisar Wakilai ta Nigeria ta kafa wata kwamiti ta musamman ta tsaro a yau Laraba

- An dora wa kwamitin alhalin binciko hanyoyin magance kallubalen tsaro a Nigeria

- Kwamitin da ta kunshi shugabannin majalisa da mambobi daga dukkan jihohin zata fitar da rahoto cikin sati uku

Majalisar Wakilai na Tarayyar Najeriya, a ranar Laraba ta kafa wata kwamiti mai karfi da zai bullo da hanyoyin magance kallubalen rashin tsaro da ke adabar kasar ya kuma gabatar da rahotonsa cikin makonni uku.

Kakakin Majalisar Wakilai, Hon. Femi Gbajabiamila ne ya sanar da kafa kwamitin inda ya ce hakan na cikin abubuwan da aka amince da su yayin taron shugabannin kwamitin a safiyar ranar Laraba kafin fara zaman majalisa.

DUBA WANNAN: Jerin ƙasashen Afirka 7 da kuɗaɗensu ya fi daraja a 2021

Yanzu-Yanzu: Majalisar Wakilai Ta Kafa Kwamiti Mai Ƙarfi Kan Tsaro
Yanzu-Yanzu: Majalisar Wakilai Ta Kafa Kwamiti Mai Ƙarfi Kan Tsaro. Hoto: @TheNationNews
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Sayyada Rabi'atu Harun: Matar Da Ta Yi Waƙar 'Mai Daraja Annabi Ma'aiki' Ta Rasu

Kakakin ya ce kwamitin za ta kunshi dukkan shugabannin majalisar da kuma mambobi 30 daga jihohin Nigeria 30, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Ya ce idan kwamitin ta kammala bincikenta za a mika wa Shugaba Muhammadu Buhari domin aiwatarwa.

Idan za a iya tunawa kallubalen tsaro kamar yan ta'adda, yan bindiga, masu garkuwa da makasa na addabar mutane kuma an gaza samun mafita.

"Kwamitin za ta fara aiki nan take kuma za ta dauki kimanin watanni biyu ko uku kafin ta bada rahoton ta domin a mika wa shugaban kasa. Kwamitin ta kunshi mambobi 30 da shugabannin majalisa," in ji Gbajabiamila.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Source: Legit

Tags:
Online view pixel