Sayyada Rabi'atu Harun: Matar Da Ta Yi Waƙar 'Mai Daraja Annabi Ma'aiki' Ta Rasu
- Fitacciyar mai wakokin yabon Annabi, Sayyada Rabi'atu Harun ta riga mu gidan gaskiya
- Rabi'atu Harun ta rasu ne a ranar Talata a unguwar Rigasa da ke jihar Kaduna
- Sharif Mu'az, mijinta ya tabbatar da rasuwarta inda ya ce mutuwarta ya girgiza shi
Allah ya yi wa Sayyada Rabi'atu Harun, matar da ta yi fiice wajen wakokin yabon Manzon Allah, Annabi Muhammad (SAW) ta riga mu gidan gaskiya.
BBC ta ruwaito cewa mijinta, Sharif Mu'az ya ce ta rasu ne a ranar Talata 16 ga watan Maris a Rigasa Kaduna bayan jinya na makonni uku.
DUBA WANNAN: Jerin ƙasashen Afirka 7 da kuɗaɗensu ya fi daraja a 2021
An yi jana'izarta bisa koyarwar addinin musulunci a yammacin ranar Talata kamar yadda mijinta ya bayyana.
Sharif Mu'az ya ce ya yi matkukar girgiza sakamakon rasuwar matarsa da ya bayyana a matsayin mutumiya mai hali na gari kana ya yi addu'ar Allah ya jikanta da rahama.
Marigayiyar ta rasu ta bar 'ya'ya biyu a duniya.
KU KARANTA: Bayan shekaru 5 da sakinta, mata ta koma gidan tsohon mijinta ta lakaɗawa amaryarsa duka
Cikin wakokin da ta yi na yabon annabi akwai 'Mai daraja Annabi Ma'aiki', Zahra'u Fadima, Shukriyya Sajida, Sayyidin Nasi Karimi da sauransu.
Jama'a da dama masu son wakokinta da sauran musulmi sun yi jimamin rasuwarta a dandalin sada zumunta inda suka yi addu'ar Allah ya jikanta da rahama ya gafarta mata.
Wani mai amfani da shafin Twitter Isa Usman ya yi alhinin rasuwar Sayyada Rabi'atu yana mai addu'ar Allah ya jikanta ya yi mata rahama ya karbi bakuncinta domin darajar Annabi Muhammadu Rasulullah.
A wani rahoton daban kun ji cewa, rundunar yan sandan jihar Kano ta kwantar da jama'a hankula game da wasu bakin mutane tare da rakuma da suka bayyana a wasu sassan jihar.
Daily Nigerian ta gano cewa mazauna jihar sun ankarar da yan sanda kan bakin mutanen da suka yada zango a wasu sassan jihar.
Wasu mazauna garin suna zargin matafiyar sun iso jihar ne domin aikata laifi da sunan fataucin kanwa.
Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.
Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.
Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.
Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu
Asali: Legit.ng