Jerin ƙasashen Afirka 7 da kuɗaɗensu ya fi daraja a 2021

Jerin ƙasashen Afirka 7 da kuɗaɗensu ya fi daraja a 2021

Mutane da dama sun san irin kudaden da ake kashewa a wasu kasashen Afirka amma ba kowa bane ya san daraja kudaden. Don haka, Legit.ng ya kawo muku kasashen Afirka 7 da kudadensu ya fi na saura daraja.

Jerin ƙasashen Afirka 7 da kuɗaɗensu ya fi daraja a 2021
Jerin ƙasashen Afirka 7 da kuɗaɗensu ya fi daraja a 2021. Hoto: @Bigmozel
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Nasara daga Allah: Sojoji sun kashe 'yan Boko Haram 41, sun ceto mutum 60 a Borno

Ga jerin kasashen Afirka bakwai da kudadensu ya fi daraja.

1. Dinar ta kasar Libya (1 USD - 1.43 LYD)

Dinar ta kasar Libya ce kudi mafi daraja a nahiyar Afirka. Dalar Amurka na dai-dai da Dinar na Libya 1.43

2. Dinar na kasar Tunisia (1USD - 2.90 TND)

Wannan ne kudi na biyu wurin daraja a nahiyar Afirka. Dinar na Tunusia 2.90 na dai-dai da Dallar Amurka 1. Libya kasa ce da ke Arewacin Afirka.

3. Cedi ta kasar Ghana (1USD - 5.75 CEDI)

Ghana kasa ce da ta dade tana aiki kan kudin kasarta domin kara masa daraja.

4. Dirhami na kasar Morocco (1USD - 9.87 Mad)

Dirhami na kasar Morocco ke biye da Cedi na kasar Ghana. Morocco kasa ce da ke Arewacin Afirka

5. Pula na kasar Botswana (1USD - 11.86 Pula)

Botsawana ce kasa ta biyar da ke da kudi mafi daraja a nahiyar Afirka, kasar da ke yankin kudancin Afirka tana da yawan mutane kimanin miliyan 2.3 a cewar kidayar kasar ta shekarar 2019.

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: 'Yan Najeriya miliyan 23 ba su da ayyukan yi, in ji NBS

6. Nafka ta kasar Eritrea (1 USD - 15.00 ERN)

Nafka ta kasar Eritrea ce kudi na shida a jerin kudade mafi daraja a nahiyar Afirka.

7. Fam na kasar Misra (Egypt) (1 USD - 15.75 EGP)

Fam na kasar Egypt ce kudi na bakwai a jerin kudade mafi daraja a Afirka.

A wani rahoton daban kun ji cewa, rundunar yan sandan jihar Kano ta kwantar da jama'a hankula game da wasu bakin mutane tare da rakuma da suka bayyana a wasu sassan jihar.

Daily Nigerian ta gano cewa mazauna jihar sun ankarar da yan sanda kan bakin mutanen da suka yada zango a wasu sassan jihar.

Wasu mazauna garin suna zargin matafiyar sun iso jihar ne domin aikata laifi da sunan fataucin kanwa.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Online view pixel