Iskilu Wakili: Bafulatanin da 'yan OPC suka kama a Oyo ya ce babu laifin da ya aikata
- Mutumin da yan OPC suka kama a jihar Oyo kan zargin garkuwa da mutane da fashi ya musanta zargin
- A ranar Lahadi ne yan kungiyar ta yarabawa na OPC ta tafi gidan Wakili ta kama shi ta danka hannun yan sanda
- A halin yanzu Wakili na hannun yan sanda bayan an dawo da shi daga asibiti inda rundunar yan sanda ta ce duk mai hujjar cewa ya aikata laifi ya gabatar da ita yanzu
Iskilu Wakili, mutumin da ake zargi da garkuwa da mutane da tada zaune tsaye ya bar asibiti zuwa hedkwatar rundunar yan sanda da ke Eleyele a Ibadan, The Nation ta ruwaito.
Yan kungiyar yarabawa ta Oodua Peoples Congress (OPC) a ranar Lahadi ne suka kama shi suka mika shi ga yan sanda inda kwamishinan yan sanda Ngozi Onadeko ta bada umurnin a kai shi asibiti.

Asali: Twitter
DUBA WANNAN: Rundunar 'yan sanda ta yi magana kan wasu mutane masu raƙuma da suka ɓulla a Kano
An kuma kama wasu mutanensu uku tare da shi wadda a halin yanzu suna amsa tambayoyin jami'an tsaro.
Da ya ke magana da manema labarai da taimakon masu tafinta, Wakili ya bada labarin cewa yana zaune a gidansa ne kwatsam sai ya ji hayaniyar mutane.
Ya yi magana da harshen hausa/fulatanci a yayin takaitaciyyar hirar da aka yi da shi da manema labarai.
Ya musanta zargin da ake masa na aikata laifi, inda ya kallubalanci wadanda ke zargin su gabatar da hujojjinsu.
Ya ce bai dade da dawowa daga Cotonou ba inda ya tafi don a yi masa magani.
KU KARANTA: Jam'iyyar APC ba ta tausayin ƴan Nigeria, in ji Sule Lamido
Ya tabbatar da cewa yan OPC sun kama shi sun kai shi caji ofis na Ayete inda suka mika shi ga yan sanda amma bai ce sun doke shi ba.
Wakil ya ce shi kansa masu garkuwa sun taba sace yaransu biyu kuma sai da ya biya kudin fansa.
Da ta ke magana da manema labarai, kwamishinan yan sanda, Ngozi Onadeko ta ce duk wani da ke da hujja kan wanda ake zargin ya zo ya gabatar domin a bincika.
Ta kara da cewa mambobin OPC da aka tsare suma suna amsa tambayoyi.
Onadeko ta ce an gurfanar da wadanda aka kama kan rikicin Shasha sannan ta ce mutane su dena alakanta laifi da kabila.
Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.
Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.
Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.
Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu
Asali: Legit.ng