Jam'iyyar APC ba ta tausayin ƴan Nigeria, in ji Sule Lamido

Jam'iyyar APC ba ta tausayin ƴan Nigeria, in ji Sule Lamido

- Alhaji Sule Lamido, tsohon gwamnan jihar Jigawa ya ce jam'iyyar APC mai mulki ba ta da hangen nesa

- Tsohon gwamnan ya kara da cewa APC ba ta da tausayi kuma ba ta jin kan yan kasa kawai abinda ta sa a gaba shine mulki

- Tsohon gwamnan ya yi wannan jawabin ne yayin kaddamar da ayyukan titi a jihar Rivers da gwamna Nyesome Wike ya yi

Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido ya yi zargin cewa jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki bata da hangen nesa, tausayi da jin kai, Daily Trust ta ruwaito.

Da ya ke jawabi yayin kaddamar da aikin titin Rumuji, Ibaa, Obelle Isokpo a karamar hukumar Emouha na jihar Rivers, a ranar Litinin, Lamido ya bayyana jam'iyyar APC a matsayin tarin mutane da ke cike da fushi, hassada da gaba.

Jam'iyyar APC ba ta tausayin 'yan Nigeria, in ji Sule Lamido
Jam'iyyar APC ba ta tausayin 'yan Nigeria, in ji Sule Lamido. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Mutum 10 sun riga mu gidan gaskiya sakamakon hadarin mota a Bauchi

Ya ce ayyukan sake fasalin filayen jiragen sama, farfado da layyukan dogo da sauye-sauyen da wannan gwamnatin ke alfahari da su duk ayyukan da jam'iyyar PDP ta kirkira ne.

"A lokacin da suka samu mulki, ba su da shirye-shirye. Ba su da tsari; abinda suka sa a gaba kawai shine su kori gwamnatin PDP saboda muna aiki; muna da tsari, saboda muna aiki tukuru, saboda muna da tausayin mutane," in ji shi.

"Su APC ba za su iya tunani ba. Ba su da hangen nesa, ba su da tausayi, kawai mulki suke nema kuma yanzu mulkin na wahal da su, saboda ba su rike amanar mulkin ba."

KU KARANTA: Ranar mata ta duniya: Fadar shugaban ƙasa ta lissafa mata 50 da ke riƙe da madafan iko a gwamnatin Buhari

Tunda farko, Gwamnan Rivers, Nyesome Wike ya ce yana gudanar da ayyukansa ne domin samar da kyakyawar yanayi da jama'ar jiharsa za su amfana da shi su nemi arziki su bunkasa.

A wani rahoton daban kunji cewa kungiyar musulmi ta Jama’atu Nasril Islam (JNI) ta ce ba za ta hallarci mukabala da gwamnarin jihar Kano ta shirya da Sheikh Abduljabbar Kabara ba, Daily Trust ta ruwaito.

An shirya yin mukabalar ne a ranar 7 ga watan Marisa tsakanin malaman Kano da Sheikh Abduljabbar da ake zargi yana yi wa Annabi Muhammad batanci cikin karatunsa.

JNI, da Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar III ke shugabanta, ta ce bata da masaniya kan matakan da aka dauka kawo yanzu don warware rashin fahimtar

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Online view pixel