Domin ceto daliban Jangebe, Gwamnan Zamfara ya nemi taimakon Auwalu Daudawa da dan Buharin Daji

Domin ceto daliban Jangebe, Gwamnan Zamfara ya nemi taimakon Auwalu Daudawa da dan Buharin Daji

- A daren Juma'a, an sace dalibai a makarantar sakandaren kwana na mata GSSS Jangebe

- Cikin yunkurin da ake na cetosu, an nemi taimakon wasu manyan yan bindigan da suka mika wuya

Domin samun nasaran ceto dalibai mata 317 da aka sace ranar Juma'a, gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya nemi taimakon tubabbun dan bindiga Auwalu Daudawa da Zakoa Buhari, ThisDay ta ruwaito.

Auwalu Daudawa ne dan bindigan da ya jagoranci satan daliban makarantan sakandaren GCSS, Kankara, a jihar Katsina.

Zakoa Buhari kuma shine dan shahrarren kasurgumin dan bindiga, Buhari Daji.

An sace dalibai a makarantar sakandaren kwana na mata GSSS Jangebe, karamar hukumar Talata Mafara, a jihar Zamfara.

Daudawa, wanda dan asalin jihar Zamfara ne ya mika wuya ga gwamna Matawalle kwanaki tara da suka wuce kuma ya ajiye makamansa tare da yaransa tare da alkawarin taimakawa gwamnan wajen yaki da yan bindiga.

Majiyoyi sun bayyana cewa Daudawa ya san yan bindigan da suka sace daliban Jangebe kuma Matawalle ya kirasa ranar Juma'a domin ya taya shi rokon yan bindigan su sake daliban.

Wata majiya ta bayyana cewa bayan haka, Matawalle ya kira Zakoa Buhari, wanda shima ya mika wuya ga hukumar ranar Alhamis da ta gabata.

KU KARANTA: Ku daina baiwa yan bindiga kudi ya na da hadari, Buhari ya gargadi gwamnoni

Domin ceto daliban Jangebe, Gwamnan Zamfara ya nemi taimakon Auwalu Daudawa da dan Buharin Daji
Domin ceto daliban Jangebe, Gwamnan Zamfara ya nemi taimakon Auwalu Daudawa da dan Buharin Daji Credit: Channels TV
Asali: UGC

DUBA NAN: Hotunan daliban Karaga bayan sun kwashe kwanaki 9 hannun yan bindiga

"Gwamnan na Zamfara na neman taimako daga wadannan tubabbun yan bindigan saboda zasu iya janyo hankalin wadanda suka sace daliban su sakesu ba tare da zub da jini ba," cewar Majiyar.

"Maganar gaskiya itace Daudawa da Zakoa Buhari sun san yawancin yan bindigan nan."

"Za'a iya amfani da su wajen sakin yan matan cikin kwanciyar hankali. Shi yasa Matawalle ya kirasu," majiyar ta kara.

A bangare guda, shugaban kasan ya bayyana hakan ne ranar Juma'a yayin tsokaci kan sace dalibai mata a makarantar sakandaren GGSS Jangebe a jihar Zamfara.

Buhari ya ce sam ba zai taba amincewa da irin wannan garkuwa da dalibai da akeyi ba.

A jawabin da mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu ya saki, Buhari ya yi kira ga gwamnoni su daina baiwa yan bindiga kudade da motoci.

Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin uku yanzu tare da shararriyar jarida Legit.

Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss.

Asali: Legit.ng

Online view pixel