Yanzu-yanzu: DSS ta musanta kama Dawisu, hadimin Ganduje

Yanzu-yanzu: DSS ta musanta kama Dawisu, hadimin Ganduje

- Hukumar yan sandan farin kaya, SSS, ta musanta zargin da ake yi na cewa ta kama Salihu Tanko-Yakasai da aka fi sani da Dawisu

- Wannan zargin na cewa ne bayan batarsa tun ranar Juma'a da ake dangatawa da wani sako da ya wallafa a Twitter na sukar Shugaba Buhari da APC kan tsaro

- A bangarenta, hukumar ta SSS reshen jihar Kano ta ce Salihu abokinta ne, ba ta kama shi ba kuma bata gayyaci shi ba

Hukumar yan sandan farin kaya, SSS, reshen jihar Kano, ta musanta kama Salihu Tanko-Yakai, hadimin gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje saboda kalaman da ya yi na sukar Shugaba Muhammadu Buhari da jam'iyyar APC mai mulki, Daily Nigerian ta ruwaito.

Idan za a iya tunawa a yayin da aka sace yaran yan makaranta a jihar Zamfara, Mr Tanko Yakasai wanda ake fi sani da Dawisu, ya shafinsa na Twitter ya bayyana cewa gwamnatin APC ta gaza.

DUBA WANNAN: Ba zan yi wa ƴan bindiga afuwa ba, in ji Shugaba Buhari

Yanzu-yanzu: DSS ta musanta kama Dawisu, hadimin Ganduje
Yanzu-yanzu: DSS ta musanta kama Dawisu, hadimin Ganduje. Hoto: @daily_nigerian
Asali: Twitter

Jim kadan bayan wallafa sakon, an rasa gano inda Yakasai ya ke a cewar abokansa don haka aka fara zargin cewa jami'an yan sandan farar hula na SSS ne suka yi awon gaba da shi.

Mr Alhassan ya ce: "Ba mu kama Salihu ba, ko gayyatarsa ma ba mu yi ba, kada mu kanta shi abokin mu ne, ya kan bamu shawarwari kan muhimman batutuwa da suka shafi tsaro a Kano."

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Baku fi ƙarfin gwamnati na ba, Buhari ya gargaɗi ƴan bindiga

A bangarensa, Alhaji Tanko Yakasai, jigo a kungiyar dattawan Arewa kuma uba ga Salihu Tanko Yakasai ya tabbatar da cewa dansa (Salihu) yana tsare a hannun jami’an tsaro.

Sai dai shima bai fayyace takamaiman hukumar tsaron da ta tsare dan nasa ba.

Yakasai a wata hira ta wayar tarho da jaridar Vanguard a safiyar ranar Asabar, 27 ga watan Fabrairu, ya ce an tsare dan nasa ne tun daga ranar Juma’a lokacin da ya tafi gidan aski kuma yana kan hanyarsa ta komawa gida.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe tsawon shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Online view pixel