Yanzu-yanzu: Baku fi ƙarfin gwamnati na ba, Buhari ya gargaɗi ƴan bindiga
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gargadi yan bindiga da kakkausan murya bayan sace yan matan GGSS Jangebe a Zamfara
- Shugaba Buhari ya shaidawa yan bindigan cewa babu wata kungiyar bata gari da ta fi karfin gwamnatinsa
- A cewar shugaban kasar, ba don yan bindigan na iya amfani da yan makarantar a matsayin garkuwa ba da tuni sojoji sun gama da su
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gargadi yan bindiga da ke adabar al'umma a sassan kasar, inda ya ce gwamnatinsa za ta iya yin maganin su.
A cikin sanarwar da ya fitar, mai magana da yawun shugaban kasa Garba Shehu ya ce shugaban kasar ya nuna damuwarsa kan karuwar ayyukan bata gari.
Ya ce idan ba domin ana iya amfani da wadanda aka sace a matsayin garkuwa ba wanda zai haifar da salwatar rayyuka, da tuni jami'an tsaro sun gama da su.
DUBA WANNAN: Bayarabe musulmi bai taba mulkin Nigeria ba tun samun ƴancin kai, MURIC ta koka
Shugaban kasar ya bayyana satar ɗaruruwan ɗaliban na GGSS Jangebe a jihar Zamfara a matsayin rashin tausayi kuma ba za a amince da shi ba.
"Wannan gwamnatin ba za ta lamunci harin da yan bindiga ke kai wa yaran makaranta ba da nufin samun kudin fansa.
"Su dena bari magagi na dibansu suna ganin kamar sun fi karfin gwamnati ne. Kada su dauki kame kan da muke yi domin kare rayuwar wadanda ba su-ji-ba -ba-su-gani ba a matsayin tsoro, " in ji shi
KU KARANTA: FAAC: Jihohi 5 da suka samu kason kudi mafi tsoka a shekarar 2020
Shugaban kasar ya yi kira ga gwamnatocin jihohi su yi bita kan tsarinsu na sakawa yan bindiga da kudade da motoci, inda ya yi gargadin hakan na iya karfafawa wasu cigaba da kai hare-haren.
Ya shawarci jihohi da kananan hukumomi su dauki matakan samar da tsaro a makaratu da garuruwan da ke kusa da makarantun.
A wani labarin daban, ofishin mai bawa Shugaban Kasa shawara kan Tsaro da Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Isa Ali Pantami, a jiya sun sha banban kan kaddamar da fasahar sadarwa ta 5G a Najeriya, Daily Trust ta ruwaito.
Sun yi magana ne a Abuja yayin wani taro da kwamitocin Majalisar Dattawa kan Sadarwa, Kimiyya da Fasaha, da Yaki da Laifukan Yanar Gizo da Lafiya da Cututtuka masu Yaduwa suka shirya kan matsayin fasahar 5G.
A yayin da Pantami ya ce Najeriya ta shirya tsaf domin kaddamar da fasahar 5G, ofishin NSA ta nuna damuwarta kan wasu matsaloli da ke tattare da fasahar.
Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.
Ya shafe tsawon shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.
Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.
Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu
Asali: Legit.ng