Ba zan yi wa ƴan bindiga afuwa ba, in ji Shugaba Buhari

Ba zan yi wa ƴan bindiga afuwa ba, in ji Shugaba Buhari

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa ba za ta yi wa yan bindiga da ke kaiwa yan Nigeria hare-hare afuwa ba

- Buhari ya bayyana hakan ne yayin wani taro da aka gudanar da gwamnonin arewa da masu sarautun gargajiya a ranar Alhamis a Kaduna

- Shugaban kasar ya ce ya rika ya bawa shugabannin hukumomin tsaro umurnin su bullo da tsarin da za su magance yan bindigan da sauran bata gari

Shugaba Muhammadu Buhari, a ranar Alhamis, ya ce ba zai yi wa yan bindiaga da ke adabar jama'ar kasar afuwa ba, inda ya ce gwamnatinsa za ta cigaba da yaki da yan bindigan da masu garkuwa da yan ta'adda, The Punch ta ruwaito.

Shugaban kasar ya yi wannan jawabin ne yayin bude taron Kungiyar gwamnonin Arewa, Masu Sarautun gargajiya na Arewa da tawagar gwamnatin tarayya da aka gudanar a jihar Kaduna.

DUBA WANNAN: Abin da yasa muka tuba muka miƙa makamanmu, tsaffin 'yan bindigan Zamfara

Ba zan yi wa 'yan bindiga afuwa ba, in ji Shugaba Buhari
Ba zan yi wa 'yan bindiga afuwa ba, in ji Shugaba Buhari. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

Shugaban kasar da ya samu wakilcin shugaban ma'aikatan fadarsa, Farfesa Ibrahim Gambari ya ce lokaci ya yi da ya dace a dena tsangwamar wata kabila a tunkari masu laifi.

A cewarsa, kallubalen tsaro da ke adabar kasar sun kawo koma baya ga kokarin gwamnatinsa na tsamo yan kasar daga talauci don haka ya bawa shugabannin tsaro umurnin su fito da tsare-tsare na kawo karshen laifuka a kasar.

Shugaban kasar ya kuma godewa kokarin gwamnonin jihohin arewa 19 bisa kokarinsu na kawo cigaba da gina kasa musamman a irin wannan lokacin da ake fama da kallubale daban-daban.

KU KARANTA: Hotunan auren mace mai shekaru 91 da mijinta mai shekaru 71 da aka daura bayan shekaru 10 suna soyayya

Gwamnonin jihohi da suka hallarci taron sun hada da Abdullahi Ganduje na Kano, Nasir El-Rufai na Kaduna, Aminu Bello Masari na Katsina, Abubakar Badaru na Jigawa, Abdullahi Sule na Nasarawa, Mai Mala Buni na Yobe, Simon Lalong na Plateau, Aminu Tambuwal na Sokoto da Atiku Bagudu of jihar Kebbi, yayin da sauran kuma mataimakansu suka wakilce su.

Sarakunan gargajiya da suka hallarci taron sun hada da; the Sarkin Musulmi, Sa’ad Abubakar III, Shehun Borno, Umar Ibn El-Kenemi, Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero, Sarkin Ilorin, Ibrahim Sulu Gambari, Etsu Nupe, Yahaya, Sarkin Zazzau, Ahmed Nuhu Bamali, da wasu saura.

Tawagar gwamnatin tarayya ya hada da, CoS, Professor Ibrahim Gambari, Ministan Sadarwa, Lai Mohammed, Mataimakin kakakin Majalisar Wakilan Tarayya, Ahmed Wase, wanda ya wakilci Kakkain Majalisar da Sufeta Janar na Yan sanda, Mohammed Adamu da wasu saura.

A wani labarin daban, basarake mai sanda mai daraja ta daya, Olupo na Ajase-Ipo, Oba Sikiru Atanda Woleola ya riga mu gidan gaskiya, The Nation ta ruwaito.

Marigayin sarkin, ya rasu ne misalin karfe 10 na daren ranar Lahadi, 21 ga watan Fabrairun 2021 bayan fama da gajeruwar rashin lafiya a garinsa da ke Ajase-Ipo kamar yadda aka ruwaito.

Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq na jihar Kwara ya yi wa masarautar da jama'ar karamar hukumar Ajase-Ipo ta'aziyya bisa rasuwar basaraken.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe tsawon shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164