Ku yi hakuri, muna neman afuwa: Shugaban CAN ga Musulman Billiri

Ku yi hakuri, muna neman afuwa: Shugaban CAN ga Musulman Billiri

- Jagoran mabiyar addinin Kirista a Billiri ya nemi afuwan Musulman garin

- Wannan ya biyo bayan kisa da kona Masallatan da akayi a karamar hukumar

- Gwamnan jihar Gombe ya lashi takobin hukunta wadanda suka aikata hakan kuma yayi alkawarin biya diyya

Shugaban kungiyar Kiristocin Najeriya, shiyar karamar hukumar Billiri a jihar Gombe, John Joseph, ya bukaci al'ummar Musulman garin su yafe musu bisa rikicin da ya barke a garin makon da ya gabata.

John Joseph ya bayyana hakan ne ranar Laraba bayan ganawa da gwamnan jihar Gombe, Muhammad Yahaya.

Daga cikin wadanda ke hallare a zaman sune mataimakin gwamnan, Manassah Jatau; AIG na yan sanda Abubakar Abdullahi; babban Limanin Tangale da shugabar karamar hukumar Billiri, Margaret Bitrus.

Yayin jawabi ga wadanda ke hallare a zaman, shugaban na CAN ya yi alkawarin aiki da sauran jagororin addinin Kirista dake garin don tabbatar da an yi sulhu.

"Ga iyayen da suka rasa 'yayansu, muna musu jaje. Mu al'ummar Kirista muna bada hakuri. Muna bada hakuri ga Musulman da aka kona musu Masallaci," Joseph yace.

DUBA NAN: Tarzomar Billiri: Gwamnan Gombe ya yi alƙawarin tabbatar da zaman Lafiya

Ku yi hakuri, muna neman afuwa: Shugaban CAN ga Musulman Billiri
Ku yi hakuri, muna neman afuwa: Shugaban CAN ga Musulman Billiri Hoto: The Punch/Muhammad Isa Gaude
Asali: UGC

KU KARANTA: Rikicin addini a Gombe: Ba zan lamunci aikata ta'addanci a jiha ta ba, gwamna Inuwa

Rikicin Billiri

Rikicin ya biyo bayan zanga-zangar da wasu kungiyoyi suka yi ne wadanda ke zargin gwamnatin da rashin adalci a tsarin zaben sabon Mai Tangale a Billiri.

Hakanan akwai rikicin addini yayin da aka kona wuraren bautar musulmai a yankin na Billiri.

Amma a wani labarin, Inuwa Yahaya, gwamnan jihar, ya ce tsarin nadin sabon basaraken ya kasance a bayyane, kuma tashin hankalin ya faru ne daga wadanda ke son shafa wa gwamnati bakin fenti don ta zabi wani dan takararsu.

Kafin a a sanar da wanda gwamnan jihar ya zaba, wasu daga cikin mazauna yankin suka fara zanga-zangar nuna su dole a nada musu zabinsu; wanda daga bisani ya jawo tashin hankalin da ya kai ga tsare hanyar Gombe zuwa Adamawa tare kone-konen masallatai da shaguna.

Gwaman jihar ta Gombe ya fito yayi bayanin halin da ake ciki tare da bayyana matakin da ya dauka dangane da lamarin.

Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin uku yanzu tare da shararriyar jarida Legit.

Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss.

Asali: Legit.ng

Online view pixel