Rikicin addini a Gombe: An lalata kadarori a rikici kan nadin sabon sarkin Billiri

Rikicin addini a Gombe: An lalata kadarori a rikici kan nadin sabon sarkin Billiri

- Rikici ya barke a wani yankin jihar Gombe sakamakon rashin sanar sabon sarkin Tangale

- Rikicin ya haifar kona wuraren ibada tare da shagunan wasu al'umomin yankin da ma baki

- Gwamnan jihar ya sanya dokar hana fita a yankin zuwa wani lokacin da ba a sanar da budewa ba

Rikicin ya biyo bayan zanga-zangar da wasu kungiyoyi suka yi ne wadanda ke zargin gwamnatin da rashin adalci a tsarin zaben sabon Mai Tangale a Billiri.

Hakanan akwai rikicin addini yayin da aka kona wuraren bautar musulmai a yankin na Billiri.

Amma a wani labarin, Inuwa Yahaya, gwamnan jihar, ya ce tsarin nadin sabon basaraken ya kasance a bayyane, kuma tashin hankalin ya faru ne daga wadanda ke son shafa wa gwamnati bakin fenti don ta zabi wani dan takararsu.

Kafin a a sanar da wanda gwamnan jihar ya zaba, wasu daga cikin mazauna yankin suka fara zanga-zangar nuna su dole a nada musu zabinsu; wanda daga bisani ya jawo tashin hankalin da ya kai ga tsare hanyar Gombe zuwa Adamawa tare kone-konen masallatai da shaguna.

KU KARANTA: Ba kudin fansa 'yan bindiga suke nema ba kafin su sako daliban Kagara, in ji Sheikh Gumi

Rikicin addini a Gombe: An lalata kadarori a rikici kan nadin sabon sarkin Billiri
Rikicin addini a Gombe: An lalata kadarori a rikici kan nadin sabon sarkin Billiri Hoto: The Punch/Muhammad Isa Gaude
Asali: UGC

Gwaman jihar ta Gombe ta fito yayi bayanin halin da ake ciki tare da bayyana matakin da ya dauka dangane da lamarin.

Yake cewa: "Ya ku 'yan uwana, duk kuna sane cewa bayan rasuwar Mai Martaba, marigayi Abdu Buba Maisheru II, kuma daidai da dokokin da al'adun da muka shimfida, mun sanya ayyukan zabar sabon Mai Tangle," in ji shi. .

“Tsarin, wanda ya kasance a bayyane kuma ba tare da wata tsangwama ba, ya haifar da tura mutane uku da aka ba da shawara ta hanyar sarakunan gargajiya na Tangale, daga cikinsu zan zabi dan takarar da zai cike kujerar Mai Tangle kamar yadda doka ta tanada."

Gwamnan ya ce batun maye gurbin wani al'amari ne na Tangale tare da jihar Gombe kuma dukkanin wadannan mutane ukun da aka ba da shawarar sun cancanci sarautar Tangale ne saboda nasabarsu da masarautar Mai Tangale.

Ya ce ta hanyar tarihi, kuma kamar yadda tsarin mulkin Najeriya ya tanada, addini ba shi ne mizani ba wajen zaben sabon Mai Tangale ko wani ofishin gwamnati game da hakan.

Gwamnan ya kuma sanya dokar hana fita ta sa’o’i 24 a yankin don dakile yaduwar rikici.

Ya ce gwamnati na rufe duk wani shawara kan sabon Mai Tangale har sai yadda al'amuran suka daidaita ga al'ummomin da abin ya shafa.

KU KARANTA: Ta yiwu a sako dalibai da ma'aikatan GSSS Kagara yau Lahadi, in ji Gumi

A wani labarin, Gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahaya, ya ce jihar Gombe itace jihar da ke da mafi yawan wuraren kiwo a Afirka, jaridar Punch ta ruwaito.

Yahaya ya bayyana hakan ne a ranar Juma'a, yayin da yake karbar bakuncin Ministan jiha na Aikin Gona, Mustapha Shehuri, wanda ya je jihar don kaddamar shirin bayar da kayan gona ga kananan manoma na amfanin gona 14 don rage illar cutar COVID-19.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel