Rikicin addini a Gombe: Ba zan lamunci aikata ta'addanci a jiha ta ba, gwamna Inuwa
- Gwamnan jihar Gombe Inuwa Yahaya ya tabbatar da wanzuwar zaman lafiya a jiharsa
- Ya shaidawa baki masu sha'awar shiga jihar cewa babu sauran hayaniya a cikin jihar
- Ya kuma yabawa masu ruwa da tsaki wajen tabbatar da zaman lafiya a yankin Billiri
Wadanda ba ‘yan jihar Gombe ba da ke zaune a Jihar musamman wadanda ke cikin karamar Hukumar ta Billiri da rikici ya rutsa da su an ba su tabbacin jajircewar gwamnati ga tsaron rayukansu da dukiyoyinsu, Nigerian Tribune ta ruwaito.
An shawarci al'ummomin da ke zaune su ci gaba da harkokinsu na halal ba tare da wata fargaba ba ko cin mutuncin wani muddin suka ci gaba da kasancewa masu bin doka da oda.
Gwamnan jihar, Muhammad Inuwa Yahaya ne ya bayar da wannan tabbacin a lokacin zaman sasantawa da shugabannin al’ummomi daban-daban mazauna jihar ta Gombe biyo bayan rikicin da ya barke yayin zanga-zangar lumana ta matasa da mata a karamar hukumar Billiri.
A cewar Gwamnan, ba shi da wani hakki a matsayinsa na Gwamna na keta hakkin kowa tunda ya rantse zai kare dukkan mutanen jihar ba tare da tsoro ko fifiko ba na sashe ko bangarancin addini da siyasa ba.
KU KARANTA: CBN da wasu za su haɓaka tsarin gudanar da kasuwar Bitcoin
Gwamnan ya bayyana zanga-zangar ta tashin hankali a Billiri da cewa abin kyama ne kuma abu ne da za a iya kauce masa idan har mutane za su kwantar da hankula tare da ba shi damar aiwatar da ayyukan da tsarin mulki ya ba shi a matsayinsa na Gwamnan Jihar.
Inuwa Yahaya ya bayyana cewa “Ba zan yi wasa da kowane irin aikin ta'addanci ba.
"Zaman lafiyar ku yana matukar damuna kuma mun yi duk mai yiwuwa don tabbatar da cewa ba a kai wani harin ramuwar gayya ba," in ji shi yayin da yake yaba wa 'yan sanda da sauran jami'an tsaro kan kokarin da suka yi na kwantar da tarzomar.
A nasa martanin, Mashawarci na Musamman ga Gwamnan kan Hulda tsakanin al’ummu, Cif Cornelius Ewuzie, ya gode wa gwamnan kan matakin da gwamnati ta dauka na gaggawa na kwantar da tarzomar.
Ya kuma yi alwashin kasancewa a bayan gwamnan a duk kokarinsa na wanzar da jihar cikin lumana.
KU KARANTA: Babu wanda ya mallaki AK-47 a cikinmu, Manoma sun caccaki gwamna Lalong
A wani labarin, Shugaban kasa, Manjo janar Muhammadu Buhari (mai ritaya), a ranar Lahadin da ta gabata ya yi nadamar cewa ’yan Najeriya sun zubar da jini sosai kan batutuwan da za a iya warware su cikin lumana.
A cewar wata sanarwa daga babban hadiminsa na musamman kan harkokin yada labarai, Garba Shehu, shugaban ya yi magana yayin da yake mayar da martani game da rikice-rikicen da ke faruwa a jihar Gombe wanda ya samo asali daga rikicin basaraken Billiri.
Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.
Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.
A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.
Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez
Asali: Legit.ng