Da duminsa: Bamu san adadin dalibai matan da aka sace a GGSS Jangebe ba, gwamnatin Zamfara

Da duminsa: Bamu san adadin dalibai matan da aka sace a GGSS Jangebe ba, gwamnatin Zamfara

- Yan bindiga sun sace dalibai mata a karamar hukumar Talata Mafara

- Wannan shine karo na uku da za'a sace dalibai a makarantun kwana

- A baya gwamnatin jihar ta kulle makarantun kwana goma a Zamfara

Gwamnatin jihar Zamfara ta ce bata san adadin dalibai matan da aka sace daga makarantar gwamnatin mata na GGSS Jangebe ba.

Legit Hausa ta ruwaito yadda yan bindiga suka kwashe dalibai mata daga makarantar misalin karfe daya na daren Juma'a.

Rahotanni daga kafafen yada labarai sun ce an sace dalibai sama da 300.

Kwamishanan labaran jihar Zamfara, Alhaji Sulaiman Tunau Anka, ya bayyana cewa ba'a san ainihin adadin daliban da aka sace ba, Daily Trust ta ruwaito.

"Har yanzu bamu san ainihin adadin daliban da aka sace ba. Jami'an tsaro sun bazama neman yan bindigan," yace.

"Sun shiga makarantan da ababen hawa. Wasu cikin yan mata da kafa suka taka. Muna lura da lamarin kuma muna kokarin ganin cewa mun ceto daliban."

DUBA NAN: Satar 'yan makaranta: Hadimin Ganduje yace Buhari ya kawo karshen ta'addanci ko yayi murabus

Da duminsa: Bamu san adadin dalibai matan da aka sace a GGSS Jangebe ba, gwamnatin Zamfara
Da duminsa: Bamu san adadin dalibai matan da aka sace a GGSS Jangebe ba, gwamnatin Zamfara Hoto: ChannelsTV
Asali: UGC

DUBA NAN: Dalla-dalla: Yadda za a samu tallafin bashin FG ga masu kananan sana'o'i

Wasu Iyaye da 'yan uwan ɗaliban da aka sace a makarantar sakandare ta GGSS Jangebe sun bayyana sun kusta cikin daji domin ceto 'yayansu da aka sace.

BBC Hausa ta ce wasu daga cikin iyayen sun shaida mata cewa su fa ba zasu jira gwamnati ba, sun shiga daji bin sahun yaransu domin cetosu daga hannun yan bindigan.

Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin uku yanzu tare da shararriyar jarida Legit.

Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss.

Asali: Legit.ng

Online view pixel