Dalla-dalla: Yadda za a samu tallafin bashin FG ga masu kananan sana'o'i

Dalla-dalla: Yadda za a samu tallafin bashin FG ga masu kananan sana'o'i

Wanne kokari gwamnatin Najeriya ke yi domin ganin ta dishe illar da annobar korona ta yi wa 'yan Najeriya da kasuwancinsu?

Wannan tambayar ta kasance a bakin mutane masu yawa saboda yadda muguwar annobar ta kawo matsala ga lafiya a fadin duniya kuma ta durkusar da tattalin arzikin kasashe.

Domin amsa wadannan tambayoyi, gwamnatin Najeriya ta sanar da manyan shirye-shiryenta kashi biyu na tallafi masu amfani. Sune:

1. Guaranteed Off-take Stimulus Scheme (GoS)

2. The General MSME Grant

A wannan rubutun, Legit.ng ta yi bayanin wadannan shirye-shiryen da kuma yadda za a samesu kamar yadda bayanai daga gwamnatin tarayya suka nuna.

KU KARANTA: Shekau ya magantu a kan tashin bama-bamai a Maiduguri da kwace gonarsa

Dalla-dalla: Yadda za a samu tallafin bashin FG ga masu kananan sana'o'i
Dalla-dalla: Yadda za a samu tallafin bashin FG ga masu kananan sana'o'i. Hoto daga Femi Adesina
Source: Facebook

1. Guaranteed Off-take Stimulus Scheme (GoS)

Wannan shirin an kafa shi ne domin bada kariya ga matsakaita tare da kananan masana'antu. Kamar yadda sunan ya nuna, an yi shirin ne domin a tabbatar da cewa an tallafawa matsakaita da kananan masana'antu.

Masana'antu matsakaita da kanana 100,000 ne za su amfana da wannan shirin.

Jihohin da za su amfana da tallafin

1. Lagos - 3,880

2. Kano - 3,280

3. Abia - 3,080

4. Sauran jihohin (Kowacce) - 2,640

Yadda za a nema kuma a samu tallafin GoS

1. Dole ne mai nema ya kasance dan Najeriya.

2. Dole mai nema ya kasance yana da rijista da CAC

3. Dole mai nema ya kasance yana da BVN da asusun banki.

4. Dole mai nema ya kasance yana da a kalla ma'aikata 2

5. Dole mai nema ya shirya samar da kayayyaki karkashin NAFDAC da SON.

Za a iya neman wannan tallafi a adireshin yanar gizo kamar haka: www.survivalfund.gov.ng

2. General MSME Grant

A wannan shirin za a baiwa kowanne mutum daya 50,000 domin habaka sana'arsa. Mutum 100,000 ne a fadin jihohin za su samu tallafin.

Yadda za a iya samun tallafin General MSME

1. Dole mai nema ya kasance dan Najeriya.

2. Dole ne mai nema ya kasance yana da rijista da CAC.

3. Dole ne mai nema ya kasance yana da BVN tare da asusun banki.

Jihohin da za su amfana da tallafin

1. Lagos - 3,880

2. Kano - 3,280

3. Abia - 3,080

4. Sauran jihohin (Kowacce) - 2,640

KU KARANTA: 'Yan bindiga daga saman bishiya sun sheke dan sanda, sun raunata wasu 3 a Neja

A wani labari na daban, diyar tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, Dr. Fatima Atiku Abubakar ta karyata ikirarin cewa ta yi sabunta rijistar zama cikakkiyar 'yar APC.

A wata takarda da ta fitar da kanta kuma ta saka hannu sannan ta baiwa manema labarai a ranar Laraba, Dr.Fatima ta ce zamanta 'yar APC a baya saboda bukatar gwamnatin Bindo na jihar Adamawa ne, Vanguard ta wallafa.

"Akasin rahotanni da ke yawo, ban sabunta rijistar APC ba. A 2015 lokacin da aka nada ni kwamishinan lafiya ta jihar Adamawa yasa na koma jam'iyyar mai mulki. Hakan ya zama dole in zan yi aikin."

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Source: Legit.ng

Online view pixel