Iyayen dalibai matan da aka sace a Zamfara sun shiga daji ceto 'yayansu

Iyayen dalibai matan da aka sace a Zamfara sun shiga daji ceto 'yayansu

- Karo na uku, tsagerun yan bindiga sun yi awon gaba da daliban makarantan kwana a Najeriya

- Wannan na zuwa mako guda bayan awon gaba da dalibai maza a jihar Neja

- Iyaye sun yanke shawaran bin sahun yaransu domin ceto su

Wasu Iyaye da 'yan uwan ɗaliban da aka sace a makarantar sakandare ta GGSS Jangebe sun bayyana sun kusta cikin daji domin ceto 'yayansu da aka sace.

BBC Hausa ta ce wasu daga cikin iyayen sun shaida mata cewa su fa ba zasu jira gwamnati ba, sun shiga daji bin sahun yaransu domin cetosu daga hannun yan bindigan.

"Gaba ɗaya garin Jangebe ne muka tasan ma ɓarayin, ko mu dawo da ranmu ko a kashe mu," a cewar wani da aka sace ƙannensa biyu.

"An ce mana an gan su ('yan bindiga) suna tafiya da yaran a cikin daji, saboda haka mutunen garin Jangebe kusan 3,000 sun fito sun ce za su bi sahunsu."

DUBA NAN: Satar 'yan makaranta: Hadimin Ganduje yace Buhari ya kawo karshen ta'addanci ko yayi murabus

Iyayen dalibai matan da aka sace a Zamfara sun shiga daji ceto 'yayansu
Iyayen dalibai matan da aka sace a Zamfara sun shiga daji ceto 'yayansu
Source: Twitter

DUBA NAN: Gwamnatin Zamfara ta tabbatar da sace dalibai mata da yan bindiga suka yi

Mun kawo muku rahoton cewa yan bindiga sun yi awon gaba da dalibai mata sama da 200 a makarantar sakandaren kwana dake garin Jangebe, karamar hukumar Talata Mafara, jihar Zamfara.

Majiyoyin sunce an sace wadannan dalibai ne misalin karfe daya na dare.

Wasu yan asalin garin biyu sun bayyanawa Legit Hausa cewa anyi awon gaba da kannensu mata.

Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin uku yanzu tare da shararriyar jarida Legit.

Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss.

Source: Legit.ng

Online view pixel