Da duminsa: 'Yan bindiga sun tare motar kudi, sun kwashe makuden kudade

Da duminsa: 'Yan bindiga sun tare motar kudi, sun kwashe makuden kudade

- Wasu 'yan bindiga sun tare motar kudi inda suka diba iyakar yadda za su iya a jihar Delta

- Lamarin ya faru a ranar Talata wanda ganau suka tabbatar da cewa sun fito ne daga daji

- Tsabar ruwan wutar da suka sakarwa motar yasa ta tsaya tare da jami'an tsaron da ke tafe

A ranar Talata ne 'yan bindiga suka kai wa motar kudi hari a Ubulu-Okiti a kan babbar hanyar Benin zuwa Asaba a karamar hukumar Aniocha ta arewa a jihar Delta.

Kamar yadda Vanguard ta wallafa, 'yan bindigan sun kai 10 kuma sun bayyana daga wani daji ne bayan hango motar kudin kuma suka dinga harbe-harbe har sai da motar kudin da masu rakiyarta suka tsaya.

Wata majiya mai karfi wacce ta jajanta yadda 'yan fashin suka yi nasarar kwashe kudin motar, ta ce sun kashe fasinja daya mace.

KU KARANTA: Tsohon shugaban DSS ya bayyana inda Gumi ya gana da 'yan bindigan Neja

Yanzu-yanzu: 'Yan bindiga sun kaiwa motar kudi farmaki a jihar Delta
Yanzu-yanzu: 'Yan bindiga sun kaiwa motar kudi farmaki a jihar Delta. Hoto daga @Vanguardngrnews
Source: UGC

Majiyar da ta bukaci a adana sunanta ta kasa tabbatar da yadda 'yan bindigan suka kwashe kudin kuma suka tsere amma ta ce fashin ya haddasa cunkoson ababen hawa a kan babban titin.

A yayin jajanta yadda masu ababen hawa, fasinjoji da mazauna kauyukan da ke kusa da wurin suka dinga neman mafaka, majiyar ta ce an dauka dogon lokaci kafin jama'a su fito koda aka gama fashin.

A yayin da aka tuntubi mukaddashin kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Bright Edafe, ya tabbatar da aukuwar lamarin amma bai tabbatar da mutuwar fasinjan ba.

KU KARANTA: Nasara daga Allah: Sojin Najeriya sun tarwatsa nakiyoyin da Boko Haram suka sa a Marte

A wani labari na daban, tsohon mataimakin daraktan hukumar tsaro ta farin kaya, Dennis Amachree a ranar Litinin ya yi bayanin cewa jami'an tsaron da aka bai wa umarnin ceto yaran Kagara basu yi musayar wuta da su bane saboda gudun rasa rayuka.

Amachree wanda ya sanar da hakan a hirar da aka yi da shi a Channels TV ya ce 'yan bindigan za su iya yin garkuwa da mutanen da ke hannunsu idan jami'an tsaro suka bude musu wuta.

Ya kara da cewa fitaccen malamin, Sheikh Ahmad Gumi, ya hadu da 'yan bindiga a dajin Neja domin tattaunawa kan sakin malamai da daliban kwalejin kimiyya ta Kagara a kusa da wurin zaman sojoji, Daily Trust ta wallafa.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Source: Legit.ng

Online view pixel