Tsohon shugaban DSS ya bayyana inda Gumi ya gana da 'yan bindigan Neja
- Dennis Amachree, mataimakin tsohon daraktan DSS ya ce an ki sakarawa 'yan bindiga wuta ne saboda gudun rasa rayuka
- Ya ce babban malami Sheikh Gumi ya samu ganawa da 'yan bindiga ne kusa da mazaunin dakarun sojin Najeriya
- Ya ce an tarar da 'yan bindiga sama da 700 a wuri daya dauke da makamai yayin tattaunawar da suka yi
Tsohon mataimakin daraktan hukumar tsaro ta farin kaya, Dennis Amachree a ranar Litinin ya yi bayanin cewa jami'an tsaron da aka bai wa umarnin ceto yaran Kagara basu yi musayar wuta da su bane saboda gudun rasa rayuka.
Amachree wanda ya sanar da hakan a hirar da aka yi da shi a Channels TV ya ce 'yan bindigan za su iya yin garkuwa da mutanen da ke hannunsu idan jami'an tsaro suka bude musu wuta.
Ya kara da cewa fitaccen malamin, Sheikh Ahmad Gumi, ya hadu da 'yan bindiga a dajin Neja domin tattaunawa kan sakin malamai da daliban kwalejin kimiyya ta Kagara a kusa da wurin zaman sojoji, Daily Trust ta wallafa.
KU KARANTA: Kyawawan hotunan zukekiyar 'yar gwamnan Bauchi yayin da ta zama cikakkiyar likita
Ya ce, "Idan ka ga 'yan bindiga haka, idan suna da yawa, za ka yanke shawarar ka shiga cikinsu ne ko ka tsaya. Domin wani lokaci suna da wadanda suka yi garkuwa da su kuma za su iya yin garkuwa da su.
"Idan aka shiga, akwai yuwuwar a samu barna. Toh ban san kwamandojin da ke yankin ba kuma ban san me suke ciki ba. Amma ina da tabbacin basu kalmashe kafafunsu ba."
Kamar yadda yace, an bukaci jami'an tsaro da su ajiye makamansu kafin su shiga cikinsu.
KU KARANTA: Da duminsa: Makasan haya sun aike da hadimin gwamna lahira
A wani labari na daban, wasu 'yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun yi awon gaba da Alhaji Ibrahim Ahmed mai shekaru 91.
Dattijon shine dagacin kauyen Kunduru da ke karamar hukumar Kankia ta jihar Katsina.
Wani mazaunin yankin ya ce an sace dagacin ne a daren Juma'a yayin da 'yan bindiga suka tsinkayi gidan basaraken da ke Kunduru kuma suka yi awon gaba da shi.
Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.
Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.
Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa
Asali: Legit.ng