Hotunan takalman mijin Ngozi Okonjo-Nweala ya janyo cece-kuce

Hotunan takalman mijin Ngozi Okonjo-Nweala ya janyo cece-kuce

- Tsoffin hotunan tsohuwar ministan kudi kuma shugaban WTO, Dr Ngozi Okonjo-Iweala sun bai wa jama'a mamaki

- Hotunan sun bayyana inda take tare da mijinta yayin da basu da wasu shekaru masu yawa amma suna cike da farin ciki

- Mutane da yawa sun jinjina musu na dadewa da suka yi, wasu kuwa takalman da ke kafar mijin suka dinga yi wa tsokaci

Yayin da 'yan Najeriya ke ta murnar babban mukamin da Dr Ngozi Okonjo-Iweala ta samu a duniya, an ga tsohon hotunanta tare da mijinta a kafar sada zumuntar zamani.

Tsohon hoton na ma'aurata sun karade kafar sada zumuntar zamani bayan da wani @huncklechu ya wallafa su.

A abinda jama'a suka kwatanta da babbar nasarar rayuwa, an hada tsohon hoton gefe da gefe da na yanzu.

KU KARANTA: Mun zuba soyayya da mijin yayata, yanzu haka ya dirka min ciki, Budurwa na son shawara

Hotunan takalman mijin Ngozi Okonjo-Nweala ya janyo cece-kuce
Hotunan takalman mijin Ngozi Okonjo-Nweala ya janyo cece-kuce. Hoto daga @huncklechu
Asali: Twitter

'Yan Najeriya sun dinga yin tsokaci daban-daban a kan labarin soyayyarsu tare da zamansu abun kwatance.

Amma kuma masu tsokacin sun dinga magana a kan takalman da Ikemba Iweala ya saka a hoton na biyu. A cewarsu, takalmin bai nuna matsayinsa ba na yanzu, hakan ke nuna kan kan da kansa.

KU KARANTA: Ka yi murabus idan ba za ka iya shawo kan matsalar tsaro ba, CSO 43 ga Buhari

A wani labari na daban, daruruwan jama'a sun shiga sarkakiya a birane da kauyuka bayan mayakan Boko Haram sun fatattaki rundunar sojin Najeriya da ke karamar hukumar Marte ta jihar Borno kusan mako daya da ya gabata.

Majiyoyi sun tabbatarwa da Daily Trust cewa mayakan ISWAP sun kafa tutocinsu a wurare daban-daban da suka hada da wurin zama a sabuwar Marte da Kirenowa, manyan biranen karamar hukumar.

A ranar Lahadi, shugaban rundunar sojin, Manjo Janar Ibrahim Attahiru sun bada sa'o'i 48 ga rundunar Operation Lafiya Dole domin kwato Marte daga hannun 'yan ta'addan Boko Haram.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Online view pixel