Boko Haram: 'Yan ta'adda sun kafa tutocinsu a Marte, daruruwan jama'a sun shiga sarkakiya
- Jama'a masu tarin yawa sun shiga mugun hali bayan Boko Haram ta mamaye Marte
- An gano cewa hatta mayakan ISWAP sun kafa tutocinsu a karamar hukumar Marte
- A makon da ya gabata ne mayakan ta'addanci suka kori sojojin daga Marte da Ngala
Daruruwan jama'a sun shiga sarkakiya a birane da kauyuka bayan mayakan Boko Haram sun fatattaki rundunar sojin Najeriya da ke karamar hukumar Marte ta jihar Borno kusan mako daya da ya gabata.
Majiyoyi sun tabbatarwa da Daily Trust cewa mayakan ISWAP sun kafa tutocinsu a wurare daban-daban da suka hada da wurin zama a sabuwar Marte da Kirenowa, manyan biranen karamar hukumar.
A ranar Lahadi, shugaban rundunar sojin, Manjo Janar Ibrahim Attahiru sun bada sa'o'i 48 ga rundunar Operation Lafiya Dole domin kwato Marte daga hannun 'yan ta'addan Boko Haram.
KU KARANTA: Kyawawan hotunan zukekiyar 'yar gwamnan Bauchi yayin da ta zama cikakkiyar likita
Ya bada umarnin kwato Kirenowa, Kirta, Wulgo, Chikingudo, da sauran yankunan da ke kusa da karamar hukumar Marte da Ngala.
An gano cewa 'yan ta'addan sun kwace wuraren da soja suke a Marte tare da kwace manyan makamai da ababen hawa, Daily Trust ta ruwaito.
KU KARANTA: Awori: Takaitaccen tarihin kabilar da ta fara zama a jihar Legas
A wani labari na daban, COAS, manjo janar Ibrahim Attahiru ya baiwa rundunar sojin Operation Lafiya Dole sa'o'i 48 da su yi gaggawar kwato Marte daga hannun 'yan Boko Haram sannan su yi gaggawar kwace garuruwa irinsu Kirenowa, Kirta, Wulgo, Chikingudo dake karkashin karamar hukumar Marte da Ngala dake jihar Borno.
Attahiru ya bayar da wannan umarnin ne a ranar Lahadi yayin yi wa sojojin Najeriya na Super Camp 9 jawabi a Dikwa, The Nation ta tabbatar.
Ya tabbatar wa da rundunar cewa lallai yana bukatar su sanya kwazo akan aikin, kuma su yi shi cikin sa'o'i 48.
Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.
Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.
Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa
Asali: Legit.ng