Mun zuba soyayya da mijin yayata, yanzu haka ya dirka min ciki, Budurwa na son shawara

Mun zuba soyayya da mijin yayata, yanzu haka ya dirka min ciki, Budurwa na son shawara

- Budurwa tana neman shawara bayan sun yi soyayya da mijin yayarta kuma har ta samu ciki

- Yayarta tana da yara mata 3 yayin da ita ke dauke da cikin yaro namiji, babban kalubale ga 'yar uwarta

- Duk da 'yan uwa sun bukaci a sakaya lamarin, babbar yayar ta sha alwashin fallasawa domin kalubale ne gareta

Wata budurwa ta je wata kungiya a kafar sada zumuntar zamani ta Facebook mai suna "Beyond Intimacy" domin neman taimako bayan lalata da ta dinga yi da mijin 'yar uwarta kuma ta samu ciki.

Kamar yadda tace, sun yi soyayya da mijin 'yar uwarta wanda hakan yasa har ta samu ciki. A halin yanzu 'yar uwarta tana da 'ya'ya uku kuma dukansu mata.

Budurwar tace bata son tonuwar asirinta kuma haka 'yan uwansu sun bukaci yayarta ta rufe zancen amma tana so ta tona.

KU KARANTA: Awori: Takaitaccen tarihin kabilar da ta fara zama a jihar Legas

Mun zuba soyayya da mijin yayata, yanzu haka ya dirka min ciki, Budurwa na son shawara
Mun zuba soyayya da mijin yayata, yanzu haka ya dirka min ciki, Budurwa na son shawara. Hoto daga @Thenation
Asali: Twitter

Har ila yau, bata da niyyar auren shi amma tana so ta haife cikin sannan ta natsu.

Ta rubuta: "Na yi soyayya da mijin 'yar uwata amma ban san zai kai haka ba.

"A halin yanzu ina da ciki kuma namiji zan haifa. 'Yar uwata tana da yara mata uku da shi.

"Hatta 'yan uwanmu sun bukaci ta hakura kuma kada ta fallasa maganar saboda za ta zubar da mutuncin gidanmu.

"Ba son auren shi nake ba. Ina so in haihu sannan in natsu. Yayata bata jin dadi saboda yana da kudi kuma ni zan fara haifar mishi namiji.

"A gaskiya bana alfahari da abinda nayi amma na sanar da ita cewa namu ne kuma yana cikin gidanmu. Ban san yadda zan shawo kan lamarin ba.

"Bana son lamarin ya bazu har na waje su ji amma ita tana son fallasawa."

KU KARANTA: Attahiru ya ba sojin Najeriya sa'o'i 48 su kwato Marte daga hannun Boko Haram

A wani labari na daban, gagarumar arangama tsakanin Boko Haram bangaren Abubakar Shekau da mayakan ISWAP ya kawo ajalin mayakan ISWAP masu tarin yawa, HumAngle ta ruwaito.

Gagarumin fadan ya faru ne a yankinsa tsakanin iyakar Nijar da Najeriya. Al-Thabat, wata kafar yada labarai mai alaka da al-Qaida ta bayyana.

A wata takarda da Al-Thabat ta fitar, ta ce Jama’at Ahl as-Sunnah lid-Da’wah wa’l-Jihad wacce aka fi sani da Boko Haram ta halaka mayakan ISWAP a wani kauye da ake kira da Sunawa tsakanin iyakar Najeriya da jamhuriyar Nijar.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng