Gwamnan Bauchi dan ta'adda ne, yana cikin wadanda suka addabi Najeriya: Gwamna Ortom

Gwamnan Bauchi dan ta'adda ne, yana cikin wadanda suka addabi Najeriya: Gwamna Ortom

- Gwamna Ortom ya sabunta musayar kalamai tsakaninsa da gwamnan Bauchi

- Wannan karon, Ortom ya zargi Kauran Bauchi da yunkurin kashe shi

- Jam'iyyar PDP na kokarin sulhu tsakanin wadannan gwamnoninta biyu

Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, ya caccaki gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, inda ya siffanta a matsayin Fulani dan ta'ada.

Yayin hira da manema labarai a gidan gwamnatin jihar dake Makurdi ranar Litinin, Ortom, ya mayar da martani ga gwamnan Bauchi kuma ya zargeshi da hada baki da Fulani Makiyaya domin kashe shi.

"Wasu makiyaya sun aiko min wasikar cewa zasu kasheni kuma dubi ga yadda dan'uwana kuma gwamnan Bauchi yake goyon bayan rike bindigarsu, ina zargin yana cikin Fulanin da ke son kashe ni," Ortom yace.

"Yanzu na fara tunan gwamnan Bauchi na cikin kungiyar Fulani yan ta'adda da suka addabi Najeriya."

Ya yi alhinin irin kalaman da gwamnan Bauchi ke yi na nuna goyon bayansa ga Fulani Makiyaya masu shigowa daga Ghana, Nijar, Libya, dss domin kashe yan Najeriya.

Ya yi kira ga makiyaya cewa su fita daga jihar Benue su koma jihar Bauchi.

KU KARANTA: El-Rufai: Najeriya ta fi kowace kasa a duniya yawan talakawa

Gwamnan Bauchi dan ta'adda ne, yana cikin wadanda suka addabi Najeriya: Gwamna Ortom
Gwamnan Bauchi dan ta'adda ne, yana cikin wadanda suka addabi Najeriya: Gwamna Ortom
Asali: Facebook

KU KARANTA: Direbobin keke napep sun dage yajin aiki a jihar Kano

A bangare guda, uwar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta saka baki don kwantar da kuran dake tsakanin gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, da gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, kan lamarin Fulani Makiyaya.

Jam'iyyar ta yi kira ga gwamnonin biyu su yi hakuri da junansu.

Tace, "Uwar jam'iyyar @OfficialPDPNig na bada tabbacin cewa ta sanya baki cikin kurar da ta tashi tsakanin gwamnan Bauchi, Sanata Bala Mohammed, da takwararsa na Benue, Gwamna Samuel Ortom."

Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin uku yanzu tare da shararriyar jarida Legit.

Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss.

Asali: Legit.ng

Online view pixel