Shikenan: Direbobin keke napep sun dage yajin aiki a jihar Kano

Shikenan: Direbobin keke napep sun dage yajin aiki a jihar Kano

- Direbobin keke napep a jihar Kano sun janye kudirin yajin aikin da suka shiga a jiya Litinin

- Shugabannin kungiyoyin direbobin sun bada umarnin ci gaba da aiki ba tare da tsaiko a jihar ba

- Hakazalika ba a cimma dage kudin harajin N100 da gwamnati ke son su dinga biya a kowace rana

Direbobin keke napep dake yajin aiki a Kano sun dakatar da matakin kuma za su ci gaba da aiki ba tare da bata lokaci ba.

Shuwagabanin hadin kan kungiyoyin masu keke napep na Najeriya sun umarci membobinsu da su ci gaba da aiki nan take.

Shugaban kungiyar, Mansur Tanimu ne ya tabbatar da haka a ranar Talata a tattaunawarsa da Aminiya ta wayar tarho.

Ya ce wannan shawarar sakamako ne na taron da aka gudanar da yammacin Talata tsakanin hukumar KAROTA a daya bangaren, kungiyar kwadago ta Najeriya (NLC) da kungiyar su a daya bangaren.

KU KARANTA: Mata a Saudiyya sun sami 'yancin shiga aikin soja a kasar

Shikenan: Direbobin keke napep sun dage yajin aiki a jihar Kano
Shikenan: Direbobin keke napep sun dage yajin aiki a jihar Kano Hoto: Epa
Asali: UGC

“Bayan taron tattaunawar bangarorin uku da muka yi da KAROTA da NLC, mun umurci shugabanninmu a matakin Karamar Hukuma da su tattauna tare da cikin hanzari tare da dakatar da yajin aikin nan take.

"Mun gabatar da bukatunmu kuma an biya wasu daga cikinsu, za mu iya samun dukkan su ba, amma mun cimma nasarori da yawa,” in ji Tanimu.

An kira yajin aikin ne don nuna rashin amincewa da harajin N100 da gwamnatin jihar ke aiwatarwa ta kowace rana ta hannun hukumar kula da hanyoyi da hukumar kula da ababen hawa ta jihar Kano (KAROTA) da sauran batutuwa.

Sai dai, bukatarsu ta janye kudin haraji bata karbu ba domin, “Duk masu abun hawan keke napep a jihar za su rika biyan harajin N100 a kowace rana kamar yadda dokar karbar haraji ta jihar Kano ta tanada, tsara jadawalin abu na 2 na tara kudin gyaran dokar 2017." In ji kungiyar.

KU KARANTA: Jarumar fim din Dadin Kowa: Burina Nollywood da Kannywood su hada kai, in ji Stella

A wani labarin, Dangane da yadda farashin mai ya hauhawa, farashin sauka da farashin Man Motoci na Fetur (PMS) ya haura zuwa N186.33 a kowace lita, The Punch ta ruwaito.

A baya mun bayar da rahoto ne a ranar 9 ga Fabrairu cewa farashin na PMS ya tashi zuwa kusan N180 kowace lita a ranar 5 ga Fabrairu daga N158.53 kowace lita a ranar 7 ga Janairu.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel