Jam'iyyar PDP ta sa baki cikin sabanin dake tsakanin gwamna Bala na Bauchi da Ortom na Benue
- Musayar kalamai tsakanin gwamnonin jam'iyyar PDP biyu ya yi muni
- Gwamna Ortom ya siffanta gwamnan Bauchi matsayin dan ta'addan Fulani
- Ortom ya ce duk abinda ya same shi a tuhumu gwamna Bala Abdulkadir
Uwar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta saka baki don kwantar da kuran dake tsakanin gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, da gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, kan lamarin Fulani Makiyaya.
Jam'iyyar ta yi kira ga gwamnonin biyu su yi hakuri da junansu.
Tace, "Uwar jam'iyyar @OfficialPDPNig na bada tabbacin cewa ta sanya baki cikin kurar da ta tashi tsakanin gwamnan Bauchi, Sanata Bala Mohammed, da takwararsa na Benue, Gwamna Samuel Ortom."
"@OfficialPDPNig na kira ga bangarorin biyu su yi hakuri da juna saboda shugabannin jam'iyyar sun shirya zaman sulhu tsakanin gwamnonin biyu."
"PDP na kira ga gwamnatin tarayya ta dau mataki kan magance matsalar tsaron da ta addabi kasar nan,"
KU KARANTA: El-Rufai: Najeriya ta fi kowace kasa a duniya yawan talakawa
KU KARANTA: Direbobin keke napep sun dage yajin aiki a jihar Kano
Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, ya caccaki gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, inda ya siffanta a matsayin Fulani dan ta'ada.
Yayin hira da manema labarai a gidan gwamnatin jihar dake Makurdi ranar Litinin, Ortom, ya mayar da martani ga gwamnan Bauchi kuma ya zargeshi da hada baki da Fulani Makiyaya domin kashe shi.
"Wasu makiyaya sun aiko min wasikar cewa zasu kasheni kuma dubi ga yadda dan'uwana kuma gwamnan Bauchi yake goyon bayan rike bindigarsu, ina zargin yana cikin Fulanin da ke son kashe ni," Ortom yace.
Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin uku yanzu tare da shararriyar jarida Legit.
Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss.
Asali: Legit.ng