Ministan sadarwa, Isa Pantami ya zama gwarzon shekara na kungiyar Musulmai na 2020
- Dr. Isa Ali Ibrahim Pantami ya ci kyautar #MNAwards ta shekarar 2020
- Wannan karo Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani ne ya yi zarra
- Kafin Ministan, Gwamnan Borno da Sultan sun taba lashe wannan kyauta
Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Dr. Isa Ali Ibrahim Pantami, ya tashi a matsayin gwarzon musulmin Najeriya na shekarar 2020.
Jaridar Muslim News ta musulmai, ta bayyana cewa Isa Ali Ibrahim Pantami ne ya lashe kyautar musulmin shekara saboda irin hidimar da ya ke yi.
Wannan jarida wanda ta ke wallafe-wallafe a game da sha’anin addinin musulunci, ta ce Ministan ya yi zarra wajen inganta tattalin Najeriya.
Bugu da kari, Isa Ali Ibrahim Pantami, ya na kokari wajen ilmantar da al’umma game da addinin musulunci kamar dai yadda ya saba yi tun ba yau ba.
KU KARANTA: Ogundele, Delano da sauran Matasan da su ke ji da kudi a 2021
Jaridar ta bada wannan sanarwa ne a wani jawabi da ta fitar a ranar Juma’a ta bakin wanda ya shriya wannan bikin kyauta, Mista Rasheed Abubakar.
Rasheed Abubakar ya yi wa bikin da taken #MNAwards, domin a karrama zakakuran da su ka ba musulunci gudumuwa a shekarar 2020, da ta gabata.
Bayan kasancewarsa babban masanin addinin musulunci, Isa Pantami ya yi har digirin Ph.D. a jami’ar Robert Gordon da ke Aberdeen, ta kasar Ingila.
Ministan tarayyar ya gaji Mai girma gwamnan jihar Borno, Farfesa Umara Babagana Zulum, wanda ya lashe wannan kyauta da aka bada a shekarar 2019.
KU KARANTA: Manyan ayyuka 9 da ma'aikatar sadarwa ta yi a 2020
Mai alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Abubakar Saad III ne ya ci kyautar a shekarar da ta fito a 2018.
Watanni uku da su ka wuce ne ku ka ji cewa Allah madaukakin Sarki (SWT) ya yi wa wata 'yar Ministan sadarwa da tattalin arzkin zamanin rasuwa.
Isa Ali Pantami ya rasa 'yar cikinsa, Aishah Isa Ali (Amal), mai shekaru 13 da haihuwa rasuwa.
Kamar yadda Ministan ya bada sanarwa, an yi jana'izar ta a a masallacin Annur da ke unguwar Wuse 2 a babban birnin tarayya Abuja bayan an yi sallar azahar.
M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.
Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.
A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi
Asali: Legit.ng