Jerin Mashahuran Attajiran Matasa 5 da su ka fi kowa dinbin dukiya a Najeriya

Jerin Mashahuran Attajiran Matasa 5 da su ka fi kowa dinbin dukiya a Najeriya

- Akwai wasu matasa da su ke juya miliyoyin kudi a halin yanzu a Najeriya

- Miss Linda Ikeji ta na cikin matan da sa ku fi kowa arziki a Nahiyar Afrika

- Mun tattaro wasu daga cikin wadannan mutane da inda suka samu kudinsu

Duk da halin da kasa ta ke ciki a sakamakon annobar cutar COVID-19 da ta barke, akwai wasu tsiraru da kudinsu sai gaba ma ta ke kara yi.

Legit.ng ta kawo jerin mashahuran matasa 5 da yanzu babu kamarsu a Najeriya wajen juya kudi.

1. Sijibomi Ogundele

Sijibomi Ogundele mai shekara 36 shi ne kan gaba a dukiya a kasar nan. Ogundele ya na koyi ne da gwaninsa, masanin fasaha, Dr. Sujimoto Koga na wata jami’a a kasar Jafan.

KU KARANTA: Orji Ogbonnaya Orji ya zama sabon Shugaban hukumar NEITI

2. Ladi Delano

Mujallar Forbes da kanta ta san da zaman Ladi Delano. Wannan mutumi da ya kafa Bakrie Delano shi ne na biyu a jerinmu. Ana maganar darajar kamfaninsa ya haura Dala biliyan $1.

3. Igho Sanomi

Shugaban kamfanin Taleveras Group, Igho Sanomi, shi ne ya zo na uku a jerin attajiran Najeriya. Mahaifin ‘dan kasuwar tsohon jami’in ‘dan sanda ne wanda ya kai matsayin AIG.

4. Linda Ikeji

Mace guda da ta iya shiga wannan sahu ita ce Linda Ifeoma Ikeji. Shafin wannan ‘yar kasuwa ya gawurta, sannan ta mallaki gidan talabijin na Linda Ikeji, sai dai ta kai shekara 40.

Jerin Mashahuran Attajiran Matasa 5 da su ka fi kowa dinbin dukiya a Najeriya
Ladi Delano Hoto: www.answersafrica.com
Source: UGC

KU KARANTA: Attajirai 8 da su ka mallaki rabin dukiyar duniya

5. Jason Njoku

Jason Njoku mai shekara 39 shi ne ya cika wannan gurbi ‘Dan kasuwar ya yi fice ne da kamfanin Spark da ya bude Ya na cikin wadanda su ka kafa kamfanin fim dinnan na iROKOtv.

A 2019, mun kawo maku wasu manyan attajirai biyar 'yan arewa da su ke cikin masu kudin Najeriya. Na farkonsu a wannan jeri shi ne hamshin 'dan kasuwa Aliko Dangote.

Daga cikinsu akwai Abdussamada Rabiu wanda Mahaifinsa, Marigayi Khalifah Isyaku Rabiu, yana daya daga cikin manyan malamai da kuma 'yan kasuwan da aka yi a Arewa.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Source: Legit.ng

Online view pixel