Allah ya yi wa 'yar Pantami rasuwa
- Allah ya yi wa 'yar Ministan sadarwa na Najeriya Dakta Isa Ali Pantami rasuwa
- Dakta Pantami ya sanar a shafinsa na Twitter a ranar Litinin cewa 'yarsa, Aishah Isa Ali ta rasu a Abuja
- Ministan ya kara da cewa saboda wasu uzurori za a yi jana'izarta a ranar Talata a masallacin Annur da ke Abuja
Aishah Isa Ali (Amal), diyar Ministan Sadarwa ta tattalin arziki na zamani, Shiekh Isa Ali Pantami ta rasu.
Amal wacce ke da shekaru 13 a duniya ta rasu ne a ranar Litinin 23 ga watan Nuwamban 2020 kamar yadda Sheikh Pantami ya sanar ta shafinsa na Twitter.
DUBA WANNAN: Jihohi 10 mafi arziki a Najeriya
Ministan ya kuma sanar da cewa za ayi jana'izar ta a gobe (Talata) a masallacin Annur da ke Wuse 2 a Abuja bayan sallar Zuhr idan Allah ya kai mu.
Ga sakon da ministan ya wallafa.
"Inna lil Laahi wa inna ilaiHi Rajiun!
"Allah ya yi wa 'ya ta mai shekaru 13, Aishah Isa Ali (Amal) ta rasuwa ba dadewa ba.
"Saboda wasu uzurori, zai ayi mata sallar jana'iza gobe a masallacin Annur, Wuse 2, da zarar an kammala sallar Zuhr in sha Allah.
"Allah ya gafarta mata, ya jikanta da rahama."
KU KARANTA: 'Yan bindiga sun kashe masallata 5, sunyi awon gaba da liman da mutum 40 yayin sallar Juma'a a Zamfara
A wani labarin da Legit.ng ta wallafa, hukumar kwana kwana na Jihar Kano, a ranar Juma'a, ta ceto wata dattijuwa mai shekaru 80 da ta fada a cikin rijiya a Tundun Wuzurchi a Municipal a Jihar Kano kamar yadda The Punch ta ruwaito.
Mai magana da yawun hukumar kwana kwana, Malam Saidu Mohammed cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma'a, ya ce an kira hukumar daga Tundun Wuzurchi misalin karfe 6.40 daga wani Mallam Ibrahim Hussaini.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng