Yanzu-yanzu: CACOVID ta barranta kanta da gudunmawar rigakafin da BUA za ta bawa Nigeria

Yanzu-yanzu: CACOVID ta barranta kanta da gudunmawar rigakafin da BUA za ta bawa Nigeria

- CACOVID ta musanta rahoton da ke cewa kamfanin BUA zai hada kai da ita domin siyan allurar riga kafin korona

- Hakan na zuwa ne jim kadan bayan kamfanin na BUA ya fitar da sanarwar cewa zai bawa Nigeria gudun mawar rigakafin guda dubu daya

- CACOVID ta ce babu wani kamfani da mutum daya da zai iya siyan allurar rigakafin hasali ma ta hannun gwamnatin tarayya ake siya

Gammayar kungiyoyi masu zaman kansu da ke yaki da COVID-19 wato CACOVID ta nesanta kanta da sanarwar da kamfanin BUA ta fitar na cewa kamfanin na shirin siyo wa Nigeria rigakafin korona, The Cable ta ruwaito.

A sanarwar da ta fitar a ranar Litinin, kamfanin BUA ta sanar da cewa za ta siya rigakafin korona miliyan daya na kamfanin AstraZeneca ta hannun bankin Afrexim tare da hadin gwiwa da CACOVID.

DUBA WANNAN: Hotunan hatsabibin mai garkuwa da aka kama yayin da ya tafi karbar kuɗin fansa

Yanzu-yanzu: CACOVID ta barranta kanta da gudunmawar rigakafin da BUA za ta bawa Nigeria
Yanzu-yanzu: CACOVID ta barranta kanta da gudunmawar rigakafin da BUA za ta bawa Nigeria. Hoto: @thecableng
Asali: Twitter

KU KARANTA: Aljamiranci ne ya samar da Dangote, Rabiu da sauransu, in ji Adamu Garba

Sai dai a nata sanarwar, CACOVID ta musanta gudunmawar da BUA ta sanar da siyan rigakafin inda ta ce babu wani mutum ko kamfani da zai iya siyan rigakafin da kansa sai dai ta hannun gwamnatin tarayya kadai za a iya siya.

A wani labarain daban, babban malamin Kano, Shaikh Abduljabbar Nasir Kabara ya ce rufe masallacinsa da hana shi yin wa'azo da gwamnatin jihar ta yi "zalunci ne", kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito.

Malamin ya ce gwamnatin da kanta, ta bakin kwamishinan ilimi na jihar, ta tabbatar da cewa abinda ake yi masa zalunci ne amma ta dakatar da shi ba tare da bashi damar ya kare kansa ba.

Abdul-jabbar ya yi wannan jawabin ne biyo bayan rufe masallacinsa da ke makarantarsa da gwamnatin Kano ta yi a ranar Laraba gami da hana saka karuntunsa a gidajen rediyo da kafafen sada zumunta na jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel