Aljamiranci ne ya samar da Dangote, Rabiu da sauransu, in ji Adamu Garba

Aljamiranci ne ya samar da Dangote, Rabiu da sauransu, in ji Adamu Garba

- Tsohon dan takarar shugaban kasa Adamu Garba ya ce almajiranci ya samar da fitattun mutane daga Nigeria

- Cikin wadanda ya lissafa akwai babban attajirin Afirka, Aliko Dangote da kuma Alhaji Abdulsamad Rabiu

- Garba ya ce ba gaskiya bane cewa almajiranci na da alaka da ta'addanci domin ba hanyarsu daya ba duk da akwai bata garin malamai

Tsohon dan takarar shugaban kasa, Adamu Garba ya ce tsarin karatu na almajiranci da aka fi sani a arewacin Nigeria ne ya haifar da wasu shahararrun masu arziki a kasar ciki har da Aliko Dangote da wanda ya kafa kamfanin BUA, Abdul Samad Rabiu da sauransu.

Garba, wanda ya yi hira da The Punch a wata shirin kai tsaye da aka yi a karshen makon da ta gabata ya ce shima kansa a wani lokaci a rayuwansa ya yi almajiranci kafin ya yi karatun boko.

Aljamiranci ne ya samar da Dangote, Rabiu da sauransu, in ji Adamu Garba
Aljamiranci ne ya samar da Dangote, Rabiu da sauransu, in ji Adamu Garba. Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

Tsarin ya kunshi iyaye su tura yaransu su zauna tare da malamin addini don koyan karatun Al-Kurani da wasu ilimomin addinin musulunci.

DUBA WANNAN: Ba makiyaya bane suka bankawa makarantar sakandare wuta, Gwamnatin Kogi

Sai dai wasu da dama suna sukar tsarin saboda yadda ake ganin wasu almajirai cikin kaya masu dati suna barace-barace a tituna da gidaje.

Tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II na cikin fitattun yan Nigeria wadanda ke kira a dena almajiranci da ya ce yana da nasara da talauci da karancin ilimi a arewacin Nigeria.

An kuma yi zargin cewa wasu almajiran su kan kauce su shiga ayyukan bata gari kamar zama yan bindiga ko shiga kungiyoyi irin Boko Haram da wasu masu tsatsauran ra'ayi.

Amma tsohon dan takarar shugaban kasar ya ce da nufi mai kyau aka kafa almajiranci kuma tsarin ya samar da manyan yan Nigeria. Sai dai ya koka kan abinda ya kira 'gurbata' lamarin da wasu miyagun malamai suka yi inda suke aika yara su fita su yi laifi ko barna.

Garba ya kuma musanta zargin da ake yi na cewa almajiranci na da alaka da ta'addanci a arewa domin a cewarsa 'ba tsari daya su ke ba'.

KU KARANTA: Gwamna Bala Mohammed: Yadda na kusa rasa aiki na saboda Jami'ar Baze

"Idan ka kalli Dangote, mai kudin Afirka a yau, iyalansa almajirai ne. Hasali ma, a yanzu, iyalan Dantata na daga cikin wadanda ke taimakawa kungiyar almajirai a Nigeria. Akwai kimanin almajirai 10,000 a kungiyar kuma har yanzu iyalan Dantata na taimaka musu.

"Isiyaka Rabiu, mahaifinsa shine sanannen Almajiri ne. Yan gidansu almajirai ne. Hasali ma, mahaifinsa Sheikh na da almajirai. Kafin rasuwarsa, yana goyon bayan almajiranci kuma har yau yan gidan suna taimakon almajirai. Don haka almajiranci ya gina manyan mutane. Hakan na nuna akwai alheri a cikin almajiranci," a cewar Garba

A wani labarain daban, babban malamin Kano, Shaikh Abduljabbar Nasir Kabara ya ce rufe masallacinsa da hana shi yin wa'azo da gwamnatin jihar ta yi "zalunci ne", kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito.

Malamin ya ce gwamnatin da kanta, ta bakin kwamishinan ilimi na jihar, ta tabbatar da cewa abinda ake yi masa zalunci ne amma ta dakatar da shi ba tare da bashi damar ya kare kansa ba.

Abdul-jabbar ya yi wannan jawabin ne biyo bayan rufe masallacinsa da ke makarantarsa da gwamnatin Kano ta yi a ranar Laraba gami da hana saka karuntunsa a gidajen rediyo da kafafen sada zumunta na jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel