Korar Makiyaya Fulani: Ƙungiyar Arewa ta buƙaci Gwamna Abiodun ya yi murabus

Korar Makiyaya Fulani: Ƙungiyar Arewa ta buƙaci Gwamna Abiodun ya yi murabus

- Hadaddiyar Kungiyar Tuntuba ta Arewa, AUCF, ta fadawa gwamnan Ogun, Dapo Abiodun ya yi murabus

- Wannan jawabin ya fito ne daga bakin shugaban kungiyar, Alhaji Shuaibu Dansudu, a ranar Alhamis a Legas

- Kungiyar ta ce gwamnan ya gaza a kare rayuka da dukiyoyin mutanen da ke jiharsa a matsayinsa na babban mai tsaro a jihar

Hadaddiyar Kungiyar Tuntuba ta Arewa, AUCF, ta bukaci gwamnan jihar Ogun, Prince Dapo Abiodun ya yi murabus daga kujerarsa saboda abinda ta kira gazawarsa wurin kiyaye rayyuka da dukiyoyin al'ummar da ke jiharsa.

Kungiyar ta kuma yi Allah wadai ta ayyukan Sunday Adeyemo da aka fi sani da Sunday Igboho da ake zargi da lalata rugar fulani a jihar a farkon wannan makon, SaharaReporters ta ruwaito.

Korar makiyaya: Kungiyar Arewa ta bukaci gwamnan Ogun ya yi murabus
Korar makiyaya: Kungiyar Arewa ta bukaci gwamnan Ogun ya yi murabus. Hoto: @SaharaReporters
Source: Twitter

Wannan na cikin sanarwar ta kungiyar, AUCF, ta fitar ne a ranar Alhamis a Legas ta bakin shugabanta Alhaji Shuaibu Dansudu.

DUBA WANNAN: Kwamishina ya yanke jiki ya fadi ya mutu yayin gabatar da kasafin kudi a Enugu

Kungiyar ta ce, "Gwamna Abiodun ne babban mai tsaro a jihar amma abin takaici ya gaza samar da tsaro a jiharsa, har sai da ya gayyaci wani daga jihar Oyo domin ya zo ya yi masa aikinsa.

"Don haka muna kira ga gwamnan ya yi murabus daga matsayinsa domin akwai alamun ba zai iya aikin ba. Idan bai yi murabus din ba, gwamnatin tarayya ta janye jami'an tsaron da ta ba shi."

KU KARANTA: Alkali ya yanke wa matashi hukuncin daurin rai-da-rai saboda haike wa wata a Jigawa

A game da Igboho, AUCF, ta bayyana shi a matsayin dan gwagwarmaya na bogi inda ta ce yan gwagwarmaya na gaskiya ba su daukar doka a hannunsu ko kuma kai wa mutanen da ba su ji ba su gani ba hari.

A wani labarain daban, babban malamin Kano, Shaikh Abduljabbar Nasir Kabara ya ce rufe masallacinsa da hana shi yin wa'azo da gwamnatin jihar ta yi "zalunci ne", kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito.

Malamin ya ce gwamnatin da kanta, ta bakin kwamishinan ilimi na jihar, ta tabbatar da cewa abinda ake yi masa zalunci ne amma ta dakatar da shi ba tare da bashi damar ya kare kansa ba.

Abdul-jabbar ya yi wannan jawabin ne biyo bayan rufe masallacinsa da ke makarantarsa da gwamnatin Kano ta yi a ranar Laraba gami da hana saka karuntunsa a gidajen rediyo da kafafen sada zumunta na jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel