Alkali ya yanke wa matashi hukuncin daurin rai-da-rai saboda haike wa wata a Jigawa

Alkali ya yanke wa matashi hukuncin daurin rai-da-rai saboda haike wa wata a Jigawa

- An yanke wa wani matashi dan shekara 27 daurin rai da rai a Jigawa saboda haike wa wata yi wa

- An tabbatar da laifin da ya aikata tun 15 ga watan Maris na bara bayan sauraren shaidu hudu

- Babbar kotun jihar da ke zamanta a Dutse ta kuma daure wani shekara 21 a gidan yari tare da wanke wani daga irin wannan zargi

Wata babbar kotun Jihar Jigawa, da ke zamanta a Dutse ta yanke wa wani mutum dan shekara 27, Suleiman Ahmed, daurin rai da rai, bayan kama shi da laifin haike wa wata yarinya.

Kotun ta sake daure wani mutum shekara 21 a gidan yari bisa irin wannan laifi yayin da ta wanke wani daga zargin tare da sallamar shi.

Kotu ta yanke wa matashi hukuncin daurin rai-da- rai a Jigawa
Kotu ta yanke wa matashi hukuncin daurin rai-da- rai a Jigawa. Hoto: @daily_trust
Asali: UGC

A wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai hulda da jama'a na ma'aikatar shari'a, Zainab Baba Santali ta fitar, ta ce, Ahmed, dan kauyen Lutai a karamar hukumar Birnin Kudu da ke jihar, ya aikata laifin ranar 15 ga watan Maris na shekarar da ta gabata a garin Babaldu.

DUBA WANNAN: Gwamnatin Kano ta hana Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara wa'azi a jihar

Sanarwar ta kara da cewa mai laifin ya ja wata yarinya mai shekaru 11 zuwa wani kango inda ya haike mata, ta ce shari'ar, wanda babban jojin jihar, Musa Aliyu ya jagoranta, an gabatar da shaidu hudu bayan ya karyata zargin.

Daga cikin shaidun akwai kawayen yarinyar guda biyu wanda suka tabbatar da cewa sun ga mai laifin yana jan ta kango, kuma sun bi bayan su, sun kuma ga ya aikata abinda ake tuhumarsa.

KU KARANTA: Zalunta ta gwamnatin Kano ta yi, Sheikh Abduljabbar Kabara

Alkali mai sauraren karar, Musa Ubale, ya ce shaidun sun tabbatar da hujjojin su akan mai laifin kuma ya yanke masa hukuncin daurin rai da rai.

A wani labarin daban, Hukumar Kula da Makarantun Frimare, SUBEB, ta Jihar Kaduna ta sanar da sallamar wasu malaman firamare 65, kamar yadda Kamfanin dillancin labarai na NANS ya ruwaito.

An ruwaito cewa an dauke su ba bisa ka'ida ba a karamar hukumar Sanga da ke jihar kamar yadda Premium Times ta wallafa. Gwamnatin Kaduna ta kori malamai 65 daga aiki.

Jami'in binciken SUBEB, Tandat Kutama, wanda ya rike sakataren kwamitin bincike, ya tabbatar wa da NAN rahoton a Kaduna.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel